Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun sahihan bayanai daga gidajen jaridu sahihai na yadda suka tantance labarin tare da tabbatar da cewa bidiyon da labarin dake yaduwa haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa wata mata tazo daga wata duniya ɗauke da fasfon ƙasar da ba santa ba labarin ƙarya ne
Akwai wani labari dake yaɗuwa matuƙa a kafafen sada zumunta inda ake iƙirarin cewa wata ta sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na JFK dake Amurka, tana tare da fasfo ɗin wata ƙasa mai suna Torenza da babu ita a wannan duniyar da muke ciki.
Iƙirari:
Wannan labari wanda ya yaɗu a harshen Turanci amma wasu sun fassara shi suna yaɗashi a harshen Hausa.
Wani shafin Tiktok mai suna Ali Suwaga 40 ya wallafa wannan bidiyo da iƙirarin a harshen Hausa, inda yake cewa akwai wasu mutane irin mu dake rayuwa a wata duniyar ba wannan da muke ciki ba.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta fara bincike kan wannan iƙirari inda da ta sanya labarin a Google sai ya fito da cewa wasu kafafen yaɗa labarai sun tantance wato fact-checking ɗin labarin.
A cikin bincike da kafar yaɗa labarai ta NDTV ya nuna cewa bidiyo da bayanan da aka faɗa na matar duk haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
Kafar International Business Times UK International Business Times UK itama ta tantance wannan labari da cewa ƙanzan kurege ne, wato dai ƙagaggen labari ne tare da amfani da ƙirƙirarriyar basirar AI.
Itama kafar yaɗa labarai ta MSN ta tantance tare da tabbatar da cewa labarin ƙarya ne, kuma haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
Sakamakon bincike: