BindiddigiƘarya ne: Ƙasashen Burkina faso, Mali da Nijar basu...

Ƙarya ne: Ƙasashen Burkina faso, Mali da Nijar basu fara buga ƙuɗi ba, hoton AI ake yaɗawa

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa ka sa samun wannan labari a kafafen yaɗa labaran ƙasashen uku da sauran sahihan gidajen jaridu, duk da girman wannan labari. Sannan sakamakon binciken manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI ya nuna hotunan na AI ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin "Tuni dai ƙasashen AES sun fara buga kudin su" da hotunan da ka wallafa ƙarya ne.

Tun bayan ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar daga ECOWAS da kuma kafa ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel AES ake cigaba da yaɗa labarai kala-kala wasu na gaskiya wasu na ƙarya da yaudara.

Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani iƙirari na cewa; “Tuni dai ƙasashen AES sun fara buga kudin su”
A cikin wallafar akwai hotuna dake nuna shugabannin ƙasashen uku a tsaye daban wani abu dake nuna alamar buga ƙuɗi.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano wani shafin X (Twitter) mai suna @azizHaussoumi ya wallafa ɗaya daga cikin hoton da ake yaɗawa.
A wallafar da akayi a harshen Faransanci ya ce “lokaci yayi da ya kamata a fara buga kuɗi a ƙasashen AES in dai ana son cigaba.”
Haka zalika kafar tantance labarai ta Alkalanci ta sanya wannan hotuna a manhajar gano hotunan haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI inda ya nuna cewa kashi 91% na hoton haɗin AI ne.
Sannan mun duba kafafen yaɗa labarai na kasashen uku babu inda aka rawaito wannan labari.
Sakamakon bincike:
Bisa ka sa samun wannan labari a kafafen yaɗa labaran ƙasashen uku da sauran sahihan gidajen jaridu, duk da girman wannan labari. Sannan sakamakon binciken manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI  ya nuna hotunan na AI ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin “Tuni dai ƙasashen AES sun fara buga kudin su” da hotunan da ka wallafa ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar