Najeriya ta sha fama matsalar labaran karya da farfaganda na cikin gida, musamman a lokutan zabuka. ‘Yan siyasa da wasu masu bukatar cimma wasu buruka kan kirkiri labarai ko sauya labari zuwa yadda suke so wanda daga baya ana iya gano ashe ba gaskiya bane.
Farfaganda daga kasashen waje
A tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024 ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar ne suka sami kaso mafi yawa na yaɗuwar Farfaganda da labaran ƙarya daga ƙasashen waje a cewar rahoton binciken sashen harkokin waje na kungiyar Tarayya Turai EEAS.
Har ya zuwa shekarar 2025 ana cigaba da samun irin waɗannan Farfaganda da labaran ƙarya daga ƙasashen waje. Wanda yafi yaɗuwa shine na tallata shugabannin mulkin soji na ƙasashen Sahel ta amfani da bayanan ƙarya da kuma ƙirƙirrarriyar basirar AI.
Farfaganda daga waje a Najeriya
To sai dai daga tsakiyar shekarar 2024 aka fara samun yaɗuwar Farfaganda da labaran ƙarya daga ƙasashen waje ko ace waɗanda ake ɗaukar nauyi daga ƙasashen waje zuwa Najeriya wanda a turance ake kira FIMI.
Kafar African initiative
Wata kafa dake iƙirarin cewa ita ta yaɗa labarai ce mai suna African Initiative itace take yada wadannan farfaganda a kasashen Afrika wanda ta fara maida hankali da kuma ƙaimi wajen yaɗa Farfaganda da labaran ƙarya zuwa Najeriya. Wani bincike na wata kafar tantance labarai a Najeriya ya tabbatar da hakan.
Bincike ya nuna wannan kafa ta African Initiative tana da alaƙa kai tsaye da hukumar leƙen asirin Rasha.
Kafar ta African Initiative dai da farko ta fara ne a matsayin mai dillancin labarai tsakanin Rasha da Afrika, musamman wajen tallata labaran Rasha a Afrika.
Lokacin da aka ƙaddamar da kafar ta African Initiative sai da tashar talabijin ɗin ma’aikatar tsaron Rasha mai suna Zyezda tayi rahoton ƙaddamar da kafar.
Kafar har ila yau tana gaba-gaba wajen ganin an karbi ƙungiyar tsaro ta Rasha mai suna Africa Corps wacce ta maye gurbin ƙungiyar sojin haya ta Wagner.
Baban editan kafar ta African Initiative Artyom Kureyev ya kasance tsohon jami’in leken asirin Rasha wanda ƙungiyar Tarayyar Turai da kasar Burtaniya suka sanyawa takunkumi.
Yadda take yada farfaganda da labaran karya
Kafar ta African Initiative ta kware matuka wajen iya amfani da ƙirƙirrarriyar basirar AI musamman wajen hada hotuna bidiyo da kuma tura su a harsuna da dama, domin ganin abinda suke so ya karɓu ko da ba gaskiya bane.
Kafar ta kuma sha samar da shafukan ƙarya ta amfani da wani shafi mai suna newstop.Africa wajen yaɗa Farfaganda.
Abin mamaki dangane da wannan kafa ko shafi na newstop.Africa ya nuna cewa yana aiki ne daga ƙasar Nijar to amma lambar wayar da aka sanya a shafin su wanda za’a iya tuntuɓarsu ta Najeriya ce wato ta fara da +234…
Cikin irin labaran da suke yaɗawa ya haɗa da hotuna, bidiyo da akai amfani da ƙirƙirrarriyar basirar AI Sannan akwai Farfaganda da bata sunan wasu ƙasashe wanda ya haɗa da Ukraine musamman saboda yakin da akeyi tsakinin Rasha da Ukraine.
Akwai shafukan Tiktok dake yada irin wadannan labarai na karya a harshen Turanci misali wannan dake ikirarin cewa sojin Ukraine sun kashe sojojin Rasha da Mali a kasar Mali duk da cewa Ukraine bata da soja ko daya a kasar ta Mali.
A kwanakin baya ma dai gidan talabijin na Aljazeera yayi binciken ƙwaƙwaf inda ya gano yadda ƙasar Rasha ta dinga amfani da sunan ƙarya Gregoire Cyrille Dong da kuma hoton wani malamin makaranta a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya mai suna Jean Claude Sendeoli wanda ya daɗe da mutuwa aka sanya shi a matsayin kwararren masani da kuma sharhi kan tsaro da siyasa a ƙasashen Sahel da Afrika ta yamma.
Hoton mutumin daya dade da mutuwa ake amfani da shi a matsayin masanin tsaro da siyasa
Wannan bincike ya bankaɗo yadda Rashan tayi amfani da hoton mutumin wajen yaɗa Farfaganda da ƙiyayyar Faransa a ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.
Telegram da sabuwar kafar sadarwa
Kafar African Initiative na da tasha a Telegram wanda take yaɗa labaran ƙarya da tattaunawa da matasa wanda ake sanya labaran Farfaganda.
Cikin hanyoyin da akai amfani dasu wajen yaɗa da kuma samun nasarar ɗaga tutar Rasha a zanga-zangar ƙuncin rayuwa da akayi wasu jihohin arewacin Najeriya sune ta amfani da Telegram.
Kafar ta African Initiative ta samar da wata kafar sadarwa mai suna AFree wanda tuni ta buɗe ofishin wannan kafar sadarwa a Lagos.
Wannan kafar sadarwa dai tana tallata shafukan newstop.Africa da amfani da hotunan ƙirƙirrarriyar basirar AI.