Yawancin lokuta Idan akai maganar mulkin mallaka, mu anan muna tunanin cewa kasashen Afrika da wasu a Asiya ne kadai turawa suka yiwa mulkin mallaka to sai dai kash! Ba haka abin yake ba, domin kuwa akwai wasu kasashe a tsakiya da gabashin turai da suka kasance a mulkin mallaka na tsawon lokaci.
Bari mu fara da kasar Czhechia wacce aka fi sani da Czech Republic, kuma ana mata taken zuciyar Turai. Kafin shakarar 1991 dai Czhechia da Slovakia na kasa daya wanda ake kira Czhechoslovakia. Wannan kasa dai ta fuskanci yaki da mamaya daga kasar Jamus wanda yakai aka bayar dasu ga kasar Rasha wacce tayi mulkin mallaka a dauka har zuwa karyewar Tarayyar Soviet.
Yayin yakin duniya na biyu birnin Prague na kasar ta Czhechia na cikin biranen da ba’a rusa ta hanyar hare-haren bam ba duk da cewa sojin kasar a Amurka sun taba Jefa bam busa kuskure. Sojin Nazi dai sun zauna a birnin Prague, kuma babu wani takamaiman dalilin daya sanya ba’a rusa ko yiwa birnin ruwan bama-bamai ba.
Ginin ma’aikatar harkokin wajen Czhechia na cikin tsoffin gine-ginen gwamnati da ya haura shekaru dari kuma yana da tarihi wajen yadda aka gudanar da yarjejeniyoyi da dama a ciki.
Duk da matsalolin mamaya, yaki, mulkin mallaka da wannan kasa ta fuskanta daga kasar Jamus da kuma Rasha amma sun maida hankali kan cigaba.
Babban birnin kasar mai suna Prague a yanzu ya zama gurin yawon bude ido, domin akwai wani agogon da ake kira astronomical clock, tsoffin gine-gine da sauran su.
Idan ka kalli gine-genen birnin akwai husumiyoyin coci da dama to amma a yanzu haka kashi 70 na mutanen kasar basu da addini.
Kasar ta Czhechia na adawa da mamayar da Rasha keyi a Ukraine, shugaban kasar na Czhechia Petr Pavel yace saboda yadda suka dandana kudarsu yayin da Rashan tayi musu mulkin mallaka lokacin tarayyar Soviet.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Czechia na fargabar Kada Turai ta bari a mamaye ko yiwa Ukraine mulkin mallaka.
Wata kasar dake tsakiyar turai wacce itama ta sha mamaya, mulkin mallaka daga kasashe daban-daban ita ce kasar Poland.
Kasar ta Poland ta sha bakar walaha a hannun kasashen Austria da Rasha.
Yayin da kasar Rasha ke yiwa wannan kasa mulkin mallaka, mun ziyarci gidan yarin da ake ajiye duk wanda ya nuna adawa da mulkin mallaka ko tsarin mulkin kwaminisanci. Akwai yadda ake azabtar da mutane daban-daban.
Haka zalika ana aika wasu zuwa wurin da yanzu yake a Serberia inda yawanci mutane kan mutu saboda tsabagen sanyi. Duk wanda za’a kai can tsuburin ana yi masa askin gefe daya domin nuna cewa mai laifi ne daga Poland.
Birnin Warsaw shine babban birnin kasar shima yana da ganuwa kamar yadda wasu biranen kasar Hausa irin Kano suke dasu. To amma lokacin yakin duniya na biyu sojin Nazi sun rusa shi baki daya.
A yanzu dai kasar Poland itama na cikin kasashen dake adawa da mamayar da kasar Rasha keyi a Ukraine domin sunce zama karkashin mulkin mallakar Rasha kamar shiga wuta ne.
Hukumomin kasar ta Poland sunce suna iya bacci ne saboda kokarin mutanen Ukraine na yaki da Rasha, inda suke tsoron cewa Idan aka bari Ukraine ta kara fadawa mulkin mallakar Rasha suma da wasu kasashen gabashi da tsakiyar Turai basu tsira ba.
Ba kamar sauran kasashen turai da sukai mulkin mallaka a Afrika ba, ita kasar Rasha tayi nata ne a kasashe makwabtan ta.
Ko zaman rarraba kasashen Afrika da akai a kasar Jamus, ita ma Rasha na kan teburin.
