Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun bidiyo da hotuna daga shafukan fadar shugaban kasa, da kuma tabbacin cewa bidiyo da hotunan tsoffi ne wadanda aka dauka a shekarar 2023 yasa Alkalanci cewa kokarin kawar da hankali ne.
Ikirari:
Wani shafin Facebook mai suna Tijjani Tj Hamza ya wallafa wani bidiyo inda yayi ikirarin cewa;
“Kwankwaso ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tunubu, sun tattauna batun ceto Nigeria da kuma batun siyasa.”

Shima wani shafin mai suna Yahuza Abdullahi ya wallafa irin wancan bidiyo ((https://www.facebook.com/share/r/15zd5YUEyM/?))

Wani shafin na Facebook shi kuma ya wallafa hotuna tare da ikirari cewa Kwankwaso ya gana da
“Kwankwaso ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a shirye shiryensa ba komawa jamiyyar APC“

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba shafin mai magana da yawun shugaban Najeriya inda babu wata wallafa makamanciyar wannan, haka zalika babu wannan bidiyo ko hotuna a shafin Sanata Kwankwaso.
Alkalanci ta gano cewa bidiyon da ake wallafawa tare da ikirarin cewa Sanata Kwankwaso ya gana da shugaba Tinubu tsohon bidiyo ne da aka dauka a watan Yunin shekarar 2023. Kamar yadda yake a wannan bidiyo da gidan jaridar TVC ya wallafa a wancan shekarar ta 2023.
Su ma hotunan an dauke su ne a shekarar ta 2023 kamar yadda gidan jaridar BBC Hausa ta wallafa a waccen shekarar.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun bidiyo da hotuna daga fadar shugaban kasa da shafin Sanata Kwankwaso, da kuma samun tabbacin cewa bidiyo da hotunan da ake yadawa an dauke su ne a shekarar 2023 yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa kokarin kawar da hankulan mutane ne.