Tun bayan dawowar damakradiyya a shekarar 1999 za’a iya cewa samun rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa ba sabon abu bane
Za’a iya cewa an dai fara ganin tsama ko rashin jituwa tsakanin Olusegun Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar.
Rashin jituwar ta su ya fara ne daga shekarar 2003 saboda wasu zarge-zargen da Obasanjon ya yiwa Atiku.
Wannan tsamar ta su ta fito fili ne a shekarar 2006 lokacin da Obasanjo ya nuna cewa yana bukatar a kwaskware kundin tsarin mulki domin yin tazarce zuwa wa’adi na uku.

To amma a zahiri dai ba’a ga tsama tsakanin marigayi tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar’adu da Goodluck Jonathan ba.

To amma bayan rasuwar Yar’adua, an sami ‘yar tsama tsakanin Jonathan da Namadi Sambo. Domin a lokacin ne aka taba furta mukamin mataimakin shugaban kasa a matsayin Safaya taya.

Haka zalika Wannan rikici na tsakanin shugaban kasa da mataimakin sa ta kara fitowa karara a siyasance lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osibanjo a lokacin da suka sami nasarar mulkin karo na biyu wato daga shekarar 2019. A wannan lokaci ne aka dinga zargi mutanen da akaiwa lakabi da cabal sune suke mulkin kasar.
An samu zarge-zarge da dama kan nuna wari ya ga shi tsohon mataimakin shugaban kasa Osibanjo har ma wasu na ganin kamar Shugaban kasar bai yadda dashi bane yasa baya bar masa karagar mulki a lokuta da dama idan zai bar kasar.
Kamar yadda akai rashin jituwa tsakanin a gwamnatocin baya gwamnati mai ci ta Bola Tinubu da Kashim Shettima ita ma za’a iya cewa ba’a barta à baya ba domin kuwa tun ba aje ko ina ba, aka fara zarge-zargen cewa an maida Kashim Shettima saniyar ware.
A kwanakin baya ma dai akwai rahotannin da suka rawaito cewa Kashim yaki komawa sabon gidan mataimakin shugaban kasa da aka gina kuma aka kaddamar bisa zargin an sanya na’urorin daukar sautin magana, wanda ya zuwa yanzu babu wata magana ta musanta hakan daga fadar shugaban kasar.
A kundin tsarin mulkin Najeriya, ayyukan mataimakin shugaban kasar Najeriya sun hada da yin duk wasu ayyuka da shugaban kasa ya bashi, da kuma zama mukaddashin shugaban kasa wato acting president, da zama mamba a majalisar tsaro ta kasa, zama a majalisar zartarwa ta tarayya FEC, da kuma zama shugaban majalisar tattalin arzikin kasa NEC.
Ba kamar yadda wasu ke fada ba. Kundun tsarin mulki ya baiwa shugaban kasa damar tura duk wani mambar majalisar zartarwa ya wakilce shi a wasu taruka.
Akwai dai labaru kala-kala da Ke yaduwa a kafafen sada zumunta dake nuna yadda rashin fahimta tsakanin shugaban kasa da mataimakin sa Ke cigaba da kamari duk da cewa fadar shugaban kasar wanda ya hada da ofishin mataimakin shugaban kasar suka musanta wasu, yayin da wasu kuma suka yi shiru basu ce kala ba.
Ku cigaba da bibiyar kafar tantance labarai, bin diddigi da bincike ta Alkalanci a www.alkalanci.com domin kare kanku daga labaran karya.