A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin da suka amince da wani kamfanin kasuwancin kiripto mai suna Crypto Bridge Exchange Smart-Treasures wanda aka fi sani da CBEX.
Kamfanin dai yayi batan dabo ko ace ya arce duk da alkawarin daya yiwa wadanda suka sanya kudi ko hannun jari na samun kashi dari bisa dari na abinda suka sanya, wannan batan dabo ya sanya koke-koke daga ‘yan Najeriya.
Matasa da dama sun riki kasuwancin Crypto hannu bi biyu wanda hakan ke nufin akwai bukatar yin taka tsantsan wajen zuba hannun jari.
Tuni dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta tabbatar da wannan batan dabo tare da cewa ta fara bincike.
To sai dai hukumar kula da zuba hannun jari da kamfanoni ta SEC ta ce kamfanin na CBEX ba shi da rijistar gudanar da kasuwanci zuba hannun jari a Najeriya.
Shugaban hukumar SEC Emomotimi Agama ya ce “ Idan kamfani baida rijista na nufin haramtacce ne. Don haka CBEX da bai da rijista to haramtaccen kamfani ne.
Bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar ilimantar da mutane kan yadda zasu gane idan kamfani na da rijistar yin kasuwancin zuba jari ko kuwa?
Hoton shafin hukumar SEC don nuna yadda zaku duba kamfanoni masu rijista SEC CSMOS
Hoton shafin SEC CMOS dake nuna inda zaku binciki sunayen kamfanoni
Hoton shafin SEC CMOS dake nuna sakamakon binciken sunayen kamfanoni ta amfani da rubutun “First Ban”.
Hukumar SEC ita ce ke lura da kasuwar zuba hannun jari na Najeriya, sun samar da wani sashe na tantance halastattun kamfanoni mai suna SEC CMOS (capital market operator search) kuma tantance kamfanoni halastattu masu rijista kyauta ne.
Hanyoyin da zaku gano kamfani na da rijista da SEC
Ku tabbata kun tantance tare da tabbatar da cewa kamfanin zuba hannun jari na da rijista da SEC kafin ku sanya kudin ku.
Duk kamfanin zuba jari da baida rijista da SEC kamar CBEX na iya rufewa ko guduwa a kowanne lokaci wanda zai sa wadanda suka zuba hannun jari tashi ba ko sisi.