Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa an saka Najeriya a cikin jerin kasashen da za’a hana shiga Saudiyya daga ranar 13 ga Afrilu, 2025.
Cikin wata sanarwar da Alkasim Abdulkadir mataimaki na musamman kan yada Labarai da tsare-tsaren sadarwa ga Ministan Harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya fitar ya ce; “hukumomin Saudiyya sun musanta ingancin wannan takarda da ake yadawa, wacce ta ƙaryata cewa kasashe da dama, ciki har da Najeriya, Misira, Indiya, Pakistan, da wasu zasu fuskanci hana biza don shiga Saudiyya. Cibiyar kula da yawon bude ido ta Saudiyya ta tabbatar da cewa babu irin wannan umarni, kuma dokokin tafiye-tafiye na hukuma da ke aiki a halin yanzu sun shafi aikin Hajji ne kawai.”
Sanarwar ta kara da cewa, A bayani mai gamsarwa, takaita shiga Saudiyya ya shafi masu bizar yawon shakatawa ne kawai a lokacin Hajji. Wadanda ke da bizar yawon shakatawa ba su da izinin yin Hajji, shiga, ko zama a birnin Makkah daga 29 ga Afrilu zuwa 11 ga Yuni, 2025 (wanda ya dace da 01 Thul Quda zuwa 14 Thul Hijjah 1446 AH).
Bizar Hajji ce kawai takardar izinin shiga da aka amince da ita ga mahajjata a wannan lokaci.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya na kira ga jama’a da su yi watsi da wannan takardar ƙarya kuma su tabbatar da sahihancin kowace sanarwa ta tafiya daga hukumomin da abin ya shafa kafin su ɗauki mataki.
Yaɗa labaran da ba’a tabbatar da su ba na iya haifar da rudani da katse shirye-shiryen tafiya.
Don samun ingantattun bayanai, matafiya su nemi bayani daga hukumomin Saudiyya, Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, ko ofisoshin jakadanci da ke da izini.