A ranakun 12 zuwa 14 ga watan Yuni ne dai ƙasar jamhuriyyar Czech ta karɓi baƙuncin shugabannin wasu ƙasashe, kwararru a fannonin tsaro, jarida da wasu fannoni da dama a taron ƙasa da ƙasa kan tsaro a faɗin duniya.

Taron wanda shugaban ƙasar Ukraine Vladimir Zelensky ya yi jawabi kan cewa Rasha ba zata daina kai hare-hare kan Ukraine ba sai ƙasashen duniya sun matsa wa shugaban Rasha Vladimir Putin lamba.
Ya ƙara da cewa idan har ƙasashen duniya suka bari Rasha ta sami nasarar mamaye Ukraine tare da fara mulkin mallakar da take son yi to fa Babu tabbacin wacce ƙasace ta gaba a gabashin Turai.
A nasa jawabin shugaban kasar Czech Petr Pavel ya bayyana muhimmancin taron tsaro musamman ta samar da sashen tattaunawa kan batutuwa masu matuƙar muhimmanci.
Taron ya ƙara da jaddada goyon baya da kuma tabbatar da bada goyon baya ga ƙasashen gabashin Turai.
Batun matsalolin labaran ƙarya
A taron an tattauna kan barazanar labaran ƙarya da kuma amfani da ƙirƙirrarriyar basirar AI wajen Farfaganda da sauya tunanin matane a ƙasashen Turai da wasu ƙasashen Afrika.
Taron dai ya jaddada buƙatar ƙasashen Tarayyar Turai EU su maida hankali kan wayar da kan mutane kan ilimin samun sahihan labarai wato media literacy. An bayyana ƙasashen Slovakia, France da Jamus na kan gaba wajen barazanar matsalolin labaran karya daga ƙasar waje wato FIMI.
Haka zalika an bayyana hotuna da bidiyo da ake amfani da ƙirƙirrarriyar basirar AI wajen haddasa rikici da bata sunayen ƙasashe da dama.
Editan Alkalanci Alhassan Bala ya sami damar halartar taron tsaron na ƙasa da ƙasa GlobalSec 2025 a birnin Prague inda ya halarci zama kan batun labaran ƙarya da kuma batun matasa, matsalar tsaro da kuma ruwan sha.

Bala na cikin ƴan jaridun Afrika 11 da ƙasar ta Czechia ta gayyata don su halarci taron. Yayin taron ya gana da masu ruwa da tsaki kan harkokin yaƙi da labaran ƙarya daga sassan duniya.
Ya bayyana farin cikin sa na ganin cewa an gano tare da amincewa da barazanar labaran ƙarya ga zaman lafiyar duniya.
Har ila yau Editan na Alkalanci ya sami tattaunawa da shugaba ƙasar ta Czechia Petr Pavel inda ya jaddada goyon bayan yaƙi da labaran da kuma kawo harkokin cigaba a ƙasashen Afrika.


Ƙasar jamhuriyyar Czech dai na cikin ƙasashen Turai da basu taɓa yiwa kowacce kasar Afrika mulkin mallaka ba.
Kuma tana cikin ƙasashen tsakiya da gabashin Turai da suka sha baƙar wuya daga hannun Turawan ƙasar Jamus da kuma mulkin mallaka da kisa daga Rasha.

Yayin wata ganawa da ƴan jaridun daga ƙasashen Afrika 8, jagororin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Czech sun jaddada cewa akwai buƙatar ƙasashen Afrika su bi a hankali wajen alaƙa da ƙasar Rasha domin Czech na cikin ƙasashen da suka ɗanɗana kuɗarsu a hannun Rasha a shekarun baya.
