Iƙirari:
Wani labari yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta Facebook cewa yayar yariman Dubai da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE ta ce tana son shugaban ƙasar Burkina Faso, wato Kyaftin Ibrahim Traore.
Inda wasu shafuka na Hausa kamar ATV Hausa, Daily Press Hausa da sauransu suka wallafa kamar haka:
“KA JI MAZA: Shugaban ƙasar Burkina Faso ya ƙi amincewa da neman aure daga Yayar Yariman Dubai, wadda ta bayyana cewa ta kamu da sonsa ne bayan ta kalli jawabansa a kafar intanet.”

Shima wannan shafin Tiktok shima ya wallafa wannan ikirari.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike mai zurfi kan wannan ikirari. Da farko ma dai, an gano cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tana da yarima daban-daban shi kuwa labarin bai fayyace wacece ba daga ciki kuma yaushe ta furta hakan, kamar yadda tsarin labaran gaskiya suke.
Binciken ya nuna cewa duka waɗannan gimbiyoyi, da ma wasu daga cikin ‘yan uwan nasu, babu wadda ta taɓa cewa tana son shugaban ƙasar na Burkina Faso.
Har ila yau, Alkalanci ta gano cewa wani bidiyo da aka yaɗa a makon da ya gabata a manhajjar Tiktok ya ba da labarin sak da harshen Turanci, kuma ga dukkan alamu da kuma sakamakon bincike ya nuna an yi amfani da kirkirarriyar basirar AI (Artificial Intelligence) ne wajen ƙirƙirar shi wancan labarin na Tiktok. Bugu da ƙari, binciken ya tabbatar da cewa hoton da aka yaɗa ba shi da wani sahihin tushe na inda abin ya faru.
Haka zalika, Alkalanci ta duba sahihan kafafen yada labarai na ƙasashen biyu amma ba a samu wannan labari ba.
Sakamakon Bincike:
La’akari da kasa samun wannan labari a sahihan kafafen yaɗa labarai, tare da tabbacin cewa asalin labarin ya dogara ne kan ƙirƙirarren bidiyon AI kuma babu wanda ya wallafa hakan tsakanin shafukan jaridun ƙasar Burkina Faso da Dubai, Alkalanci ya yanke hukuncin cewa iƙirarin da ke yaɗuwa na cewa yayar Yariman Dubai ta bayyana soyayyarta ga Shugaba Ibrahim Traore na Burkina Faso ƙarya ne.
