Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun cewa dama ɓatanci ko ƙona litattafan addini laifi ne a ƙasar Rasha kuma hukunci mafi girma shine shekaru uku a gidan yari. Sannan shugaba Putin bai bai ƙara magana kan kalmar Alkur'ani ba tun shekarar 2023 da ya ziyarci inda aka kai hari a Stockholm. Rashin samun inda aka samo mancan iƙirari yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa shugaban ƙasar Rasha Putin ya bayyana hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi ɓatanci ga Manzon Allah SAW ko ƙona Alkur'ani mai girma ƙarya ne.
Ana samun mutane a wasu ƙasashen duniya dake yin batanci ga Annabi Muhammadu SAW ko wulaƙanta Alku’ani mai girma.
Irin wadannan abubuwa dai na janyo yin Allah wadai daga Musulmai a dukkan fadin duniya.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Wakiliya ya wallafa wani labari dake cewa shugaban ƙasar Rasha Putin ya sanya hukunci mai tsanani ga duk mutumin da aka kama shi yayi ga Annabi Muhammadu SAW, ko kuma ya ƙona Alkur’ani mai girma.

Wannan wallafa dai ta sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dubu biyu, yayi da mutane da dama sukai sharing.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa sashe na 59 na kundin dokar laifuffuka na kasar Rasha ya nuna cewa hukunci mai tsanani Capital punishment na iya faruwa ne ga idan aka samu mutum da yinƙurin kashe ɗan sanda, kashe mutum, yin ƙurin kisan kiyashi. Wannan hukunci kuma ba za a iya yanke wa mace ba. Tun shekarar 1998 ba a taɓa aiki da wannan hukunci ba saboda sanya hannu da Rasha tayi kan yarjejeniyar ƙasashen Turai.
Haka zalika a kwanakin da suka gabata ne dai babban mai shigar da ƙara na gwamnatin Rasha wato General Prosecutor ya jaddada matsayar Rasha cewa ba zata canza wannan doka ba.
Alkalanci ta tuntuɓi wasu dake yankin ƙasar ta Rasha kan wannan iƙirari inda aka tabbatar da cewa ƙona litattafan addini wanda ya haɗa da Alkur’ani ko yin ɓatanci ga wani, laifi ne a sashe na 282 dake kundin laifuffuka na ƙasar Rasha, domin an sanya tsattsauran ra’ayi da kuma haddasa tsanar wasu mutane laifi ne. Hukuncin ɓatanci ga Manzon Allah ko ƙona Alkur’ani mai girma a ƙasar Rasha mafi girman hukunci shine shekaru uku a gidan yari.
To amma tun daga shekarar 2023 shugaba Putin bai faɗi kalmar Alkur’ani a bainar jama’a. A shekarar 2023 ne dai yayi magana kan yayin da ya ziyarci Stockholm yayi Allah wadai da hari da aka kai.
Sakamakon bincike:
Bisa samun cewa dama ɓatanci ko ƙona litattafan addini laifi ne a ƙasar Rasha kuma hukunci mafi girma shine shekaru uku a gidan yari. Sannan shugaba Putin bai bai ƙara magana kan kalmar Alkur’ani ba tun shekarar 2023 da ya ziyarci inda aka kai hari a Stockholm. Rashin samun inda aka samo mancan iƙirari yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa shugaban ƙasar Rasha Putin ya bayyana hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi ɓatanci ga Manzon Allah SAW ko ƙona Alkur’ani mai girma ƙarya ne.
