Bindiddigiƙarya ne: Kotu bata yanke wa Hamdiyya Sidi hukuncin...

ƙarya ne: Kotu bata yanke wa Hamdiyya Sidi hukuncin daurin shekaru biyu ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa ƙaryata wannan labari da lauyan Hamdiyya mai suna Barista Abba Hikima yayi da kuma kasa samun labarin a sahihan gidajen jaridu tare da samun rashin daidaito a shafukan da suka yada labarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin an yankewa Hamdiyya hukuncin shekaru  2 a matsayin labarin ƙar

A cikin watan Nuwamba, 2024, Hamdiyya Sidi, ’yar shekara 18 mazauniyar Jihar Sakkwato, ta wallafa wani bidiyo inda ta soki Gwamnan jihar ta Sakkwato, Ahmed Aliyu, saboda matsalolin tsaro da kuma cin zarafin mata a jihar. Inda ta buƙaci ’yan gudun hijira da su je ofishin Gwamnan a matsayin wata hanya ta nuna rashin jin daɗinsu da abubuwan da ke faruwa.

Bayan wannan wallafar ne, Rundunar ‘Yan Sandan jihar Sakkwato ta kama Hamdiyya kuma ta tsare ta, inda suka bayyana cewa kalamanta na iya tayar da tarzoma kuma ana tuhumar ta da laifin amfani da kalaman ɓatanci.

Sai dai bayan wasu watanni da faruwar wancan al’amari, an samu wallafe-wallafe da dama daga shafuka mabambanta a kafofin sada zumunta na Facebook da X wato twitter inda masu wallafar ke iƙirarin cewa kotu ta yanke wa Hamdiyya Sidi hukuncin shekara biyu a gidan yari tare da yi mata bulala 20.

Bayan zuzzurfan bincike da Alkalanci ta yi kan labarin, ta gano an fara wallafa shi ne tun a watan Afrilu, 2025 da harshen Turanci a kafar sada zumunci ta X (wato Twitter).

Labarin karya da aka fara yadawa

Bayan yi wa labarin na ƙarya kwalliya, wasu manyan shafuka da ke da dubban mabiya sun ci gaba da wallafa labarin da harshen Hausa.

Misali;
Sokoto News da ke da mabiya 1,300

Labarin karya dake cigaba da yaduwa

Katsina News da ke da mabiya 13,000.

Labarin karya dake cigaba da faduwa

Daga fara yaɗa labarin dai zuwa yanzu an yaɗa shi sama da sau 370 daga mutane da shafuka daban daban a kafofin sada zumunta.

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntubi lauyan Hamdiyya Barista Abba Hikima inda ya bayyana wannan labari da cewa karya ne. Ya kara da bayyanawa Alkalanci cewa ya rasa me yasa ake kara yada wannan labarin karyar.

Haka zalika Alkalanci ta duba sahihan kafafen yada labarai amma ba a sami wannan labari ba.

Sannan Alkalanci ta duba yadda aka dinga cin karo na labari tsakanin shafukan da suka wallafa labarin.

Sakamakon Bincike:

Bisa ƙaryata wannan labari da lauyan Hamdiyya mai suna Barista Abba Hikima yayi da kuma kasa samun labarin a sahihan gidajen jaridu tare da samun rashin daidaito a shafukan da suka yada labarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin an yankewa Hamdiyya hukuncin shekaru  2 a matsayin labarin ƙarya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar