Hukunci: Ƙarya ne
Bisa tabbatar da cewa hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne, kasancewar mukaman dake jikin su duka daya ne, sannan an kasa samun tabbacin cewa shugaban ƙasar ta Nijar nada ƙani dake aikin soja yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarye ne.
Akwai wani hoto dake yaduwa a kafafen sada zumunta inda ake iƙirarin shugaban ƙasar Nijar Janar Abdourahmane Tiani ne da ƙaninsa. A hoton dai dukkan su sanye da kayan soji.
Wani shafin Facebook mai suna Damagaram post ya wallafa hoton inda ya sami likes sama da dari biyar.

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba hoton da kyau inda ta fara gano kura-kurai dake nuna hoton ba na gaskiya bane.
Da farko dai kayan soji da mukamin dake jikin Janar Abdourahmane Tiani shine a jikin wanda ake ikirarin ƙaninsa ne.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta sanya hoton a manhajar tantance hotuna inda sakamako ya nuna cewa kashi 89% cikin ɗari na nuna cewa hoton haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI ne.
Sannan bincike ya kasa tabbatar da cewa Janar Tiani na da ƙani na jini dake aikin soja ya zuwa yanzu.
Sakamakon bincike: