Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun wannan labari a kaf kafafen yaɗa labaran Najeriya, da kuma ƙaryata faruwar fashewar wani abu a Aso Rock Villa da Abdulaziz Abdulaziz tare da rundunar ƴan sandan Najeriya sukayi yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin an sami fashewar wani abu a Aso Rock Villa da Damagaram Post sukayi ƙarya ne.
Akwai wani iƙirari dake yaɗuwa matuƙa dangane da fadar shugaban ƙasar Najeriya Aso Rock Villa.
A ranar 19-10-2025 Wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa iƙirarin cewa; “An jiyo karar fashewar wani abu mai karfi a Aso Rock villa.”
Wannan iƙirari ya sami sama da mutane dubu ɗaya da suka tofa albarkacin baki wato comments, yayin da ɗaruruwa suka ƙara wallafa wannan iƙirarin.

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta da duba shafukan sahihan gidajen jaridu a Najeriya amma babu wannan labari.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafin ƴan sandan Najeriya nan ma babu wannan labari.
Sai kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntuɓi mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz inda ya bayyanawa Alkalanci cewa babu wani abu makamancin haka daya faru a fadar shugaban ƙasar ta Najeriya Aso Rock Villa.
Har ila yau Alkalanci ta tuntuɓi rundunar ƴan sandan Najeriya inda suka suka ƙarya ta faruwar wani mai kama da fashewa a Abuja a wannan ranar balle a fadar shugaban ƙasa.
Sakamakon bincike: