Bisa samun sahihin gidan jarida a ƙasar Malasiya mai suna Free Malaysia Today FMT daya zanta da lauyan Dr. Zakir Naik mai suna Akbedin Abdul Kadir wanda ya ƙaryata labarin. Sannan Alkalanci ta ka sa samun wata sahihiyar kafar sadarwa ko jarida data wallafa labarin. Bugu da ƙari ganin cewa Dr. Zakir Naik ya cigaba da wallafa bayanai a shafin sa na X, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin ƙarya ne.
Akwai labarai dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta dake iƙirarin cewa shahararren mai wa’azi da da’awa dan ƙasar Indiya Dr. Zakir Naik na kwance a asibiti bashi lafiya a ƙasar Malaysia.
Iƙirarin:
Wani shafin Facebook mai suna Vanguard Hausa ya wallafa wannan labari a daren ranar 10 ga watan Satumbar 2025. Shafin ya rubuta labarin kamar haka;
“ YANZU-YANZU: Rahotanni Na Cewa Ankwantar Da Fitaccen Malamin Addinin musulunci Sheikh Zakir Naik A Wani Asibiti A Kasar Malesiya Cikin Mawuyacin Hali
Al’ummar musulmai Ku tayashi da Addu’a
Ku Turawa Yan uwa SU sanyashi acikin Addu’a.”
Cikin awanni 17 wallafar ta sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dubu goma sha ɗaya, sannan sama da mutum dubu biyu sukai sharing.
Haka zalika wani shafi mai suna A T V Hausa shima ya wallafa labarin a ranar 11 ga watan Satumbar 2025 inda alamu suka nuna ya kwafa ne kai tsaye daga Vanguard Hausa. Mutane sama da dubu ɗaya da ɗari biyar ne suka tofa albarkacin baki wato comments, yayin da sama da mutane dayri biyu da casa’in sukai sharing cikin awanni 7 da wallafa wa.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba tare da bincika sahihan gidajen jaridu a ƙasar Malasiya da India amma babu wacce ta tabbatar da wannan labarai.
Kafafen labaran Indiya
Ƙasar Indiya dai na neman Dr. Zakir ruwa a jallo bisa zarge-zarge da dama da suka haɗa da ta’addanci. Wasu kafafen jaridun Indiya sun rawaito yadda ake yaɗa jita-jitar cewa ya kamu da cutar HIV yana asibiti. Amma sun tabbatar babu wani tabbacin labarin, sun ƙara da cewa babu wata sahihiyar kafar yada labarai data rawaito labarin.
Kafafen labaran Malasiya
To sai dai kafar yada labarai a kasar Malasiya mai suna Free Malaysia Today FMT ta rawaito cewa labarin ƙarya ne.
Domin kuwa Lauyan Shaikh Zakir Naik mai suna Akbedin Abdul Kadir musanta labarin tare da cewa zugi ta malle ce kawai.
Labarin da gidan jaridar FMT ta rawaito na karya cewa an kwantar da Dr. Zakir Naik
Haka zalika Alkalanci ta duba shafin X (Twitter) din Dr. Zakir Naik inda ta ga cewa ya cigaba da wallafa abubuwa a shafin sa kamar yadda ya saba.
Hoton shafin X din Dr. Zakir Naik an wallafa abubuwa
Sakamakon bincike:
Bisa samun sahihin gidan jarida a ƙasar Malasiya mai suna Free Malaysia Today FMT daya zanta da lauyan Dr. Zakir Naik mai suna Akbedin Abdul Kadir wanda ya ƙaryata labarin. Sannan Alkalanci ta ka sa samun wata sahihiyar kafar sadarwa ko jarida data wallafa labarin. Bugu da ƙari ganin cewa Dr. Zakir Naik ya cigaba da wallafa bayanai a shafin sa na X, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin ƙarya ne.