Hukunci: Ƙarya ne
Bisa ka sa samun wannan labari a kafafen yaɗa labaran ƙasashen uku da sauran sahihan gidajen jaridu, duk da girman wannan labari. Sannan sakamakon binciken manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI ya nuna hotunan na AI ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin "Tuni dai ƙasashen AES sun fara buga kudin su" da hotunan da ka wallafa ƙarya ne.
Tun bayan ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar daga ECOWAS da kuma kafa ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel AES ake cigaba da yaɗa labarai kala-kala wasu na gaskiya wasu na ƙarya da yaudara.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani iƙirari na cewa; “Tuni dai ƙasashen AES sun fara buga kudin su”
A cikin wallafar akwai hotuna dake nuna shugabannin ƙasashen uku a tsaye daban wani abu dake nuna alamar buga ƙuɗi.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano wani shafin X (Twitter) mai suna @azizHaussoumi ya wallafa ɗaya daga cikin hoton da ake yaɗawa.
A wallafar da akayi a harshen Faransanci ya ce “lokaci yayi da ya kamata a fara buga kuɗi a ƙasashen AES in dai ana son cigaba.”
Haka zalika kafar tantance labarai ta Alkalanci ta sanya wannan hotuna a manhajar gano hotunan haɗin ƙirƙirarriyar basirar AI inda ya nuna cewa kashi 91% na hoton haɗin AI ne.
Sannan mun duba kafafen yaɗa labarai na kasashen uku babu inda aka rawaito wannan labari.
Sakamakon bincike:
Bisa ka sa samun wannan labari a kafafen yaɗa labaran ƙasashen uku da sauran sahihan gidajen jaridu, duk da girman wannan labari. Sannan sakamakon binciken manhajar gano hotunan ƙirƙirarriyar basirar AI ya nuna hotunan na AI ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin “Tuni dai ƙasashen AES sun fara buga kudin su” da hotunan da ka wallafa ƙarya ne.
