A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya ɗauke da sa hannun shugaban hukumar kula da tallace-tallace ta ƙasa, Dr. Olalekan Fadolapo.
An sami shafukan da suka dinga yaurar mutane ta amfani da bidiyon AI na yadda mutane zasu sami kudi cikin sauki.
Kafin wannan talla ma, an samu wani tallan da aka yi na maganin cutar kansa wadda aka yi amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar muryar Pastor Enoch Adeboye da ta ɗan jaridar nan Seun Okinbaloye aka samar da bidiyo.
Akwai dubunnan hotuna da bidiyon shugaban kasar Burkina faso Kyaftin Ibrahim Traore da ya yaɗu kuma yake yaɗuwa a kafafen sada zumunta waɗanda suka kasance na AI ne kuma ƙarya ne.
Ana dai zargin ƙasar Rasha da wannan aiki na yaɗa bidiyo da hotunan ƙarya na ƙirƙirarrayir basirar AI ƙasashen Sahel da Afrika ta yamma musamman a harshen Ingilishi, Faransanci da Hausa, wasu na fassara ƙirƙirarrun bidiyo daga turanci ko wasu yaruka zuwa harshen Hausa duk da sun kasance na ƙarya.
AI a kafafen sada zumunta na Hausa
Hakanan, ana ta samun ƙuruwar ƙirƙirarrun bidiyoyin finafinan Hausa a Najeriya waɗanda ake nuna jaruman suna rungumar juna a bainar jama’a, ɗabi’ar da ta sabawa al’adar Bahaushe.
Tun daga saɓanin da aka samu da gwamnatin Amurka da Najeriya, an samu ƙirƙirarrun bidiyoyi da hotuna daban-daban da aka samar da AI waɗanda ba su faru ba.
Cikin ‘yan shekaru kaɗan ƙirƙirarriyar basirar AI (Artificial Intelligence) ta samu karɓuwa a Najeriya fiye da yadda aka tsammata.
Yayin da abubuwan da a baya suke buƙatar ƙwararrun masana wajen sarrafawa, yanzu ana iya amfani da su har a wayoyin hannu. Kusan duk mai amfani da wayar hannu yana iya ƙirƙirar rubutu, hoto, murya da bidiyo waɗanda suke kama da na gaske. Wannan sauyi da aka samu ya buɗe sabbin damammaki na ilmantarwa, ƙirƙira da inganta ayyuka ga ‘yan Najeriya.
Sai dai kamar kullum, mafi yawanci kowanne cigaba yana zuwa da nasa ƙalubalen. Haka abin yake ga fasahar AI a Najeriya musamman ga masu amfani da harshen Hausa. Fasahar da ta yi suna wajen taimaka wa ɗalibai, ‘yan jarida, kamfanoni da sauran ɗaiɗaikun ‘yan ƙasar da ke fannin ƙirƙira, yanzu ana amfani da ita wajen samar da labaran ƙarya, hotuna, muryoyi da bidiyoyi.
Kusan a iya cewa wahalar kowane aiki raguwa take kullum saboda AI. A da yawancin mutane suna amfani da AI ne don ciyar da kai gaba, amma yanzu ana ta ƙara samun masu amfani da fasahar ta hanyar da ba ta dace ba. Cikin sauƙi mutum zai ƙirƙiri labarin ƙarya da sai an yi da gaske za a gane na ƙarya ne, ya samar da hoto ko bidiyo da zai iya ruɗar da dubban mutane. Gurɓatattun mutane yanzu sun fahimci cewa AI yana iya ba su damar yaɗa labarai na ƙarya cikin sauri.
Munanen hanyoyin da ake amfani da AI a Najeriya
Akwai hanyoyi, a ƙalla huɗu, na yadda ake amfani da AI ba yadda ya kamata ba a Najeriya. su ne kamar haka:
Labaran Ƙarya
Yanzu ana amfani da AI a ƙirƙiri cikakken labarin ƙarya a Najeriya, har a hakaito wani tushe na ƙarya a ce daga nan aka samu labarin ta yadda idan mutum bai bincika da kyau ba zai yarda.
Irin labaran nan na yaɗuwa cikin sauri fiye da yadda na gaske ke yaɗuwa, musamman a shafukan sada zumunta da ake amfani da su kamar Facebook, Tiktok, X (twitter) da zaurukan WhatApp.
Hotunan Ƙarya ko Wanda Aka Sauya Musu Fasali
AI yanzu na iya ƙirƙirar hotunan abubuwan da ba su faru ba. Zai iya sanya mutum a wani wuri da bai je ba, ko hotunan zanga-zanga, abubuwan fashewa, hayaki mai sa hawaye wato tiyagas da sauransu; wanda sai anyi da gaske ake iya gane ƙarya ce.
Ana ƙirƙirar waɗannan hotuna saboda suna saurin dugunzuma mutane, su sanya tausayi a zukata ko su haifar da tsoro, musamman idan abin ya shafi lamurran siyasa ko tsaro ko lafiya.
Ƙagaggen Bidiyo
Cigaban fasahar AI ya kai har bidiyo da muryar mutane ake iya ƙirƙira suna faɗa ko yin abin da ba su aikata ba. Da fasahar AI wadda ake kira ‘deepfake’, ana iya canza fuskoki, motsin laɓɓa da sautin murya.
Yaudarar Jama’a ta Hanyar AI
Ana amfani da AI wajen zamba. ‘Yan damfara a Najeriya na amfani da saƙonnin da AI ya ƙirƙira don yin sojan gona da jami’an tsaro, bankuna ko hukumomin gwamnati.
Yanzu haka akwai shafukan Tiktok da Facebook da dama da ake amfani dasu wajen zambatar mutane musamman ta amfani da bidiyon AI.
Illar Da Hakan Ke Haifarwa
Illar bayanan ƙarya da AI ke samarwa tana shafar rayuwar mutane a Najeriya, inda take taɓa nagartar wanda aka yi bidiyon a kansa.
Illa ga Damokradiyya
Bincike ya nuna yadda labaran ƙarya da ake hadawa ta amfani da ƙirƙirarriyar basirar AI na da tasiri wajen rugaza damokradiyya ta amfani da haddasa rikici lokacin zabe, wanda daga ƙarshe soji suyi juyin mulki ko kuma a sami yaƙin basasa.
Illa ga Mutane
Idan aka yi amfani da AI wajen ƙirƙirar maganganu, canza hotuna ko ƙagaggen bidiyo na wani mutum, galibi hakan na taɓa martabarsa kuma yana shan wuya kafin ya wanke kansa.
Shahararrun mutane za su iya fuskantar tozarci kafin a iya gyara labarin. Idan kuma mutum ba shahararre ba ne, shi ma yana fuskantar izgilanci ko tsangwama daga mutanen gari ko da an gano gaskiya daga baya.
Illa ga Al’umma
Amfani da AI wajen samar da labaran ƙarya yana sanya ƙin aminci ga jama’a gaba ɗaya. Idan mutane suka saba ganin labarai, hotuna da bidiyoyin ƙarya, za a zo gaɓar da za a daina yarda da kowane labari ko da kuwa na gaske ne.
Sannan bayanan ƙarya da AI ya ƙirƙira na iya tayar da fitina. Ƙirƙirarrun hotuna ko bidiyoyi don tada hankalin jama’a na iya haifar da rikicin addini, ƙabila ko siyasa, musamman a ƙasashe masu bambancin addini da ƙabila, kamar Najeriya.
Mafita
Duk da cewa kullum fasahar AI ƙara ingantuwa take, amma har yanzu akwai alamun da za a iya gane hoto, bidiyo ko rubutu ƙirƙirarre ne, musamman idan aka kula da kyau.
A ɓangaren hoto, za a ga yatsun hannu sun lanƙwashe ko a ga dungulumi. Kuma saɓanin yadda haske yake daidaita a hoton gaske, hoton da aka ƙirƙira da fasahar AI yana bambanta hasken wuri. Misali, hoton da aka yi da dare sai ya nuna inuwa ko a ga fitila ta bayyana a hoton da aka yi da rana; ko kuma hoton da aka yi da dare sai rana ta fito a sararin sama, da dai sauran makamantan kura-kurai.
Shi kuwa bidiyo, za a iya ganin ƙiftawar ido mara tsari saɓanin yadda ɗanAdam yake, ko a ga motsin jiki ba irin yadda mutum ya saba ba, ko sautin murya da bai dace da motsin jiki ba.
Idan ƙirƙirarriyar murya ce kuma, za a ga ta ƙi saituwa da tsari da zubin da Allah ya halicci sautin muryar mutum.
Bugu da ƙari, yana da kyau a dinga tantance asalin labari kafin yaɗawa, musamman a Najeriya inda labarai ke yawan yaɗuwa a shafukan sada zumunta.
Akwai manhajoji daban-daban na tantance gaskiyar hoto, misali ‘reverse image search’. Ko kuma abi hanya mafi sauƙi, ita ce duba manyan gidajen jaridu a Najeriya ko sun ruwaito labarin, ko a tabbatar da cewa asalin shafin da ya wallafa shi yana da inganci.
A ƙarshe, fasahar AI ba lallai ne ta zama barazana ga Najeriya ba, sai dai idan aka bar ta kara-zube, za ta zama fitina.
Idan kowanne ɗan ƙasa, kafafen watsa labarai da hukumomi suka ɗauki nauyin tantance labarai kafin yaɗawa, AI zai iya ciyar mutane gaba.
