Hukunci: Ƙarya ne
La'akari da kasa samun wani waje da ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa ta cire Tijjaniyya a matsayin ƙungiya mai alaƙa da musulunci, babu wani malamin ɗariƙar Tijjaniyya daya faɗi wani abu makamancin haka duk da girmansa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa ƙasar Saudiyya ta cire Tijjaniyya daga cikin jerin ƙungiyoyi dake alaƙa da musulunci ƙarya ne.
Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun da ke da alaka da musulunci wanda yasamu masu kallo sama da dubu Arbain a bidiyon da ya wallafa ya nuna ya dauko labarin ne daga wata kafa mai suna K.U News.

Da farko Alkalanci ta duba shafin Facebook mai suna Kano Update News inda shafin ya wallafa labarin a watan Oktoba.

Wani shafin Facebook mai suna Ministan Musabaqa ya wallafa labarin wanda ya hada da hotonsa dana Yariman Saudiyya. Ya sami Comments sama da dubu daya.
Shafuka da dama kamar wannan sun wallafa wannan labari kuma sun sami shares ɗaruruwa.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta bincika shafukan yaɗa labaran ƙasar Saudiyya amma bata gano inda aka samu wata sanarwa makamancin wannan labari ba.
Sannan babu wani kalami dake kusanci da haka daga hukumomin Saudiyya kamar yadda suka saba sanar da matakan da suka ɗauka misali sanarwa daga Ma’aikatar Hajj da Umrah.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta ƙara da duba shafukan ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta Saudiyya,
da majalisar malamai da shura inda babu inda aka ayyana cewa an cire darikar ta tijjaniya daga musulunci ba ,ko ba a dauke ta a matsayin akida mai alaka da musulunci ba.
Haka zalika duk da girman wannan labari babu wani malamin ɗariƙar Tijjaniyya daya kawo wannan labarin.
Me hukumomin Saudiyya ke gani dangane da ɗariku?
Abinda ake gani dai shine A cikin littattafan makarantu na Saudiyya, an samu rubuce-rubuce da ke sukar: wasu ayyukan Sufaye, wasu dabi’un ɗariku, wasu abubuwa da suka saɓawa fahimtar Wabahiyanci ko salafiyya.
Haka zalika a manhajar koyar da ilimin addini a Saudiyya wato (Education Curriculum) rahotanni daga Human Rights Watch sun nuna cewa littattafan Saudiyya suna ƙin wasu aƙidun Sufaye, suna bayyana su a matsayin “bidi’a” ko “kuskuren fahimta”.
Wannan yana cikin tsarin manhaja, ba hukuncin cire wata ɗarika daga musulunci ba.
Sannan Kuma Saudiyya tana bin Salafiyya/Wahhabiyya kuma wannan fahimtar ta saɓa da wasu hanyoyin Sufanci, ciki har da Tijjaniyya, Qadiriyya da dai sauransu.
Sakamakon bincike:
La’akari da kasa samun wani waje da ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa ta cire Tijjaniyya a matsayin ƙungiya mai alaƙa da musulunci, babu wani malamin ɗariƙar Tijjaniyya daya faɗi wani abu makamancin haka duk da girmansa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa ƙasar Saudiyya ta cire Tijjaniyya daga cikin jerin ƙungiyoyi dake alaƙa da musulunci ƙarya ne.
