Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun wallafa ko labarin baiwa harshen ko ƙabilar Hausa kambun zaman lafiya daga Guinness World Record, da kuma ganin cewa babu wannan kambu, tare da cewa kafin a sami kambu dole sai an nemi izinin yin abin bajintar, wanda babu inda aka rawaito wani ko wata ya nemawa ƙabilar Hausa wannan kambu, hakan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne
Akwai wani hoton alamun bada kyauta na kambun bajinta wanda ake iƙirarin cewa kundin bajinta na duniya wato Guinness World Record ne suka baiwa ƙabilar Hausa a matsayin ƙabilar data fi kowacce son zaman lafiya.
Wannan hoto dai ya yaɗu matuka a Whatsapp da kuma Facebook.
Wani shafin facebook mai suna Ibrahim Gamji ya wallafa wannan hoto.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba shafin Facebook na Guinness World Record inda babu wani abu makamancin wannan na cewa an baiwa harshen Hausa ko ƙabilar Hausa wannan kambu.
Yadda ake samun kambun bajinta na duniya
Ba kamar yadda wasu suke tunani ba, kafin Guinness World Record ya baiwa mutum kambu dole sai mutumin ya nemi izini tare da neman yin abun bajintar wanda ake cikewa a shafin na Guinness World Record. ((https://www.guinnessworldrecords.com/records/the-application-process))
Haka zalika dole sai an turawa da mutum izinin fara bajintar kafin ya fara wanda kuma zai bi matakai daki-daki wajen nuna ya cika sharuɗɗan kambun bajinta.
Alkalanci ta duba ko akwai irin wannan kambu na ƙabila mafi zaman lafiya da Guinness World Record ke bayarwa to amma ba mu samo ba.
Ƙabilar Hausa dai na iya kasancewa mai son zaman lafiya, son mutane to amma babu inda aka ga no cewa an baiwa harshen ko ƙabilar kambu.
Sakamakon bincike: