BindiddigiYadda Ake Ta Maimaita Labarin Ƙarya Kan Shugaba Putin...

Yadda Ake Ta Maimaita Labarin Ƙarya Kan Shugaba Putin Da Dokar Kare Mutuncin Alkur’ani

-

Hukunci: Ƙarya ne
Wannan wani sanannen labarin ƙarya ne da ake ta faman maimaita yaɗa shi a shafukan sada zumunta na Facebook. Masu bincike suna ayyana irin wannan labari a matsayin "Zombie Story”, wato labarin da aka riga aka tabbatar da ƙaryarsa amma yake sake tashi lokaci bayan lokaci.
“Shugaban Rasha Putin ya saka dokar hukunci mai tsanani ga duk mutumin da aka kama shi yana ɓatanci ga Manzon Allah (SAW), ko kuma ya ƙona Alkur’ani mai girma.” Wannan wani sanannen labarin ƙarya ne da ake ta faman maimaita yaɗa shi a shafukan sada zumunta na Facebook. Masu bincike suna ayyana irin wannan labari a matsayin “Zombie Story”, wato labarin da aka riga aka tabbatar da ƙaryarsa amma yake sake tashi lokaci bayan lokaci. Asalin Labarin Tushen wannan labari ya samo asali ne daga ziyarar da shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya kai babban masallacin Juma’a na birnin Derbent ranar 28 ga watan Yuni, 2023 (lokacin bikin Sallar Layya). Manufar ziyarar ita ce duba wuraren tarihi don bunƙasa harkokin yawon buɗe ido. A yayin wannan ziyara, an bai wa Putin kyautar Alkur’ani, inda ya bayyana cewa a ƙasar Rasha, mutunta Alkur’ani wajibi ne, kuma ƙona shi babban laifi ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma dokar hukunta manyan laifuka (Article 282). Sai dai, Putin bai sanya wata sabuwar doka ba a lokacin; yana magana ne kan tsohuwar dokar da ake da ita. Yadda aka Sauya Labarin Bayan wannan ziyara, wasu shafukan watsa labarai da na sada zumunta suka fara juya maganar shugaban, suna iƙirarin cewa ya “sanya sabuwar doka” ko ma “hukuncin mai tsanani” ga masu ɓatanci. • Shafin ofishin jakadancin Rasha da ke Karachi ya fitar da bayani ranar 3 ga watan Yuli, 2023, game da matsayin Rasha kan ƙona Alkur’ani a Sweden, wanda wasu suka yi amfani da shi wajen ƙirƙirar nasu labarin na ƙarya. • Shafin gidan jarida na TRT World ma ya wallafa bidiyon kalaman Putin ranar 29 ga watan Yuni, 2023, inda shugaban ke cewa ƙona Alkur’ani laifi ne a Rasha, amma ba wai an yi sabuwar doka ba ne. Sake Maimaituwar Labarin Duk da cewa wannan abu ya faru tun a 2023, wasu shafukan na Hausa sai suka ci gaba da yaɗa shi a matsayin sabon labari a farkon shekarar 2025 da ƙarshenta. Kuma suka nuna ai a shekarar ne ta 2025 abin ya faru. Ga wasu daga cikin labaran: • Shafin ATV Hausa: Ya sake wallafa labarin a watan Nuwamba, 2025, sannan ya sake maimaitawa a watan Disamba, 2025. • Shafin Diffa Studio TV: Ya sake yaɗa wannan labari a watan Oktoba, 2025. Wannan na nuna yadda shafukan sada zumunta ke amfani da labaran da suka shafi addini don samun mabiya ta hanyar yaɗa tsohon labari a matsayin sabo ko kuma su canza labarin gabaɗaya daga yadda yake a asali, wanda hakan wata hanya ce ta yaudarar jama’a.

LEAVE A REPLY

Logged in as Alhassan Bala. Log out?

Please enter your comment!

Sababbin Labarai

Ko Birtaniya da Faransa na shirin baiwa Ukraine makamin nukiliya?

Yayin da yaƙin da Rasha ke gudanarwa Ukraine ya shiga shekara huɗu akwai iƙirarai kala-kala dangane da yaƙin. Iƙirari: Wani shafin...

Me kundin tsarin mulkin Najeriya yace kan bada mukamin minista – Deji Adeyanju

Yayin da ake cigaba da takaddama kan batun ko duk wanda za a baiwa mukamin minista sai ya kasance...

Ina gaskiyar cewa Rasha bata ɗaukar ƴan Najeriya aikin soja?

Yayin da yaƙin da Rasha keyi a ƙasar Ukraine ke cika shekaru huɗu wanda ya haddasa mutuwar ɗaruruwan mutane. Tunda...

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa wani labari ɗauke da hoton wani matashi inda yayi iƙirarin...

Labarin Makiyayi mai bindiga a Kasuwar Dawanau Ƙarya ne

A ƙarshe-ƙarshen shekarar 2025 ne dai aka fara samun hare-haren yan fashin daji a wasu yankunan arewacin Kano.Iƙirari:Tun ranar...

Karanta wannan

Ko Birtaniya da Faransa na shirin baiwa Ukraine makamin nukiliya?

Yayin da yaƙin da Rasha ke gudanarwa Ukraine ya...

Me kundin tsarin mulkin Najeriya yace kan bada mukamin minista – Deji Adeyanju

Yayin da ake cigaba da takaddama kan batun ko...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar

Skip to toolbar