Fayyace abubuwaMe kundin tsarin mulkin Najeriya yace kan bada mukamin...

Me kundin tsarin mulkin Najeriya yace kan bada mukamin minista – Deji Adeyanju

-

Yayin da ake cigaba da takaddama kan batun ko duk wanda za a baiwa mukamin minista sai ya kasance yana da rijista da jam’iyyar siyasa, lauya Deji Adeyanju ya yiwa Alkalanci karin bayani kan wannan batu.
Idan ana buƙatar yiwa wannan batun cewa duk wanda zai rike ko za a naɗa muƙamin minista a Najeriya sai ya kasance yana da rijista da wata jam’iyya siyasa to sai an duba kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da akawa kwaskwarima.
Me sashe 147(5) ya ce?
Wannan sashe na 147 (5) ya ce duk wanda za a naɗa muƙamin minista a Najeriya dole sai ya cika sharuɗɗan a zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai. To amma wannan sashe ba tilo bane domin ya bayyana sashe 65(2) (b) inda yace mutum zai cancanta a zaɓe shi ɗan majalisar wakilai idan yana da jam’iyyar siyasa kuma jam’iyyar siyasa ta ɗauki nauyin sa. Wannan na iya fassaruwa matsayin duk wanda za a naɗa muƙamin minista sai yana da jam’iyyar siyasa.
To amma kundin tsarin mulkin ya ƙara da cewa ba dole sai wanda za a naɗa ministan ya kasance ɗan jam’iyyar da shugaban ƙasa ya fito ba wato ba sai ƴan jam’iyya mai ci ba kaɗai.
Da zarar an sami cikar waɗannan sharuɗɗa sashe na 141(1) ya baiwa shugaban ƙasa dama ya naɗa minista bayan sahalewar majalisar dattawa.
To amma batun dole ka zama ɗan jam’iyyar shugaban ƙasa to babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce haka.
Wannan yasa zaka iya ganin minista ya fito daga

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar cewa Rasha bata ɗaukar ƴan Najeriya aikin soja?

Yayin da yaƙin da Rasha keyi a ƙasar Ukraine ke cika shekaru huɗu wanda ya haddasa mutuwar ɗaruruwan mutane. Tunda...

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa wani labari ɗauke da hoton wani matashi inda yayi iƙirarin...

Labarin Makiyayi mai bindiga a Kasuwar Dawanau Ƙarya ne

A ƙarshe-ƙarshen shekarar 2025 ne dai aka fara samun hare-haren yan fashin daji a wasu yankunan arewacin Kano.Iƙirari:Tun ranar...

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya. Iƙirari: Akwai...

Karanta wannan

Ina gaskiyar cewa Rasha bata ɗaukar ƴan Najeriya aikin soja?

Yayin da yaƙin da Rasha keyi a ƙasar Ukraine...

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar