Masu kutse sun karbe ikon shafin X din rundunar yan sandan Tanzania a inda suka bayyana mutuwar shugabar kasar Samia Suluhu Hassan duk da cewa tana raye.
Masu kutsen dai sun wallafa sakwanni kala-kala na karya da kuma wadanda ba’a tabbatar da sahihancin su ba a safiyar ranar talata. Baya ga wallafa bayanan karya masu kutsen sunyi jawabi na kaitsayi ta shafin.
Shafin X din yan sandan na Tanzania mai mabiya Sama da dubu dari hudu da sittin. Shafin na X na cikin shafukan na ‘yan sandan ke amfani da shi wajen sanar da mutane ayyukan su.
Wannan abu dai na zuwa ne dai-dai lokacin da shugabar kasar ke takun saka da ‘yan adawa bayan kama wani jagoran adawa Tundu Lissu tare da zargin sa da cin amanar kasa.
Tuni dai ma’aikatar harkokin cikin gida ta Tanzania da rundunar ‘yan sandan suka tabbatar da kutsen tare da cewa bayanan da aka wallafa na karya ne don haka mutane suyi watsi da su.
