Hukunci: Ƙarya ne
La'akari da kasa samun wannan sanarwa ko labari a shafin ma'aikatar ilimi ta ƙasar Senegal tare da tabbacin da ma'aikatar ta bayyanawa Alkalanci ta hannun ƴar jarida a ƙasar mai suna Sofia Ba na cewa labarin ƙarya ne, kafar tantance labarai ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa labarin dake yaɗuwa cewa Senegal ta sanya Alkur'ani a cikin darasu a makarantun Senegal ƙarye ne.
Labarin sanya Alkur’ani babban darasi cikin makarantun Senegal ƙarya ne
Labaran da suka shafi addini kan kasance masu ɗaukar hankali da sosa zuciya tare da sanya mutum yarda ko rashin yarda da abinda aka faɗa ba tare da tunani ko labarin ƙarya ne ko kuma na yaudarar mutane ne.
Iƙirari:
Akwai wani shafin Facebook mai suna ATV Hausa daya wallafa wani labari ranar 25 ga watan Fabrairu shekarar 2026 cewa: “Ƙasar Senegal ta sanar a hukumance cewa za a sanya Alƙur’ani ya zama babban darasi a cikin tsarin karatun makarantun ƙasar…”
Wannan wallafa ta sami likes sama da 4,000 sai kuma shares sama da ɗari huɗu yayin da tofa albarkacin baki wato comment aka sami sama da 300.

Bincike:
Da farko kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba shafin ma’aikatar ilimin ta ƙasar Senegal inda babu wannan labari domin wallafa wato post na ƙarshe anyi shine ranar 11 ga watan Janairun wannan shekara ta 2026.

Alkalanci ta duba amma babu wani labari makamancin wannan labari dake yaɗuwa.
Haka zalika Alkalanci ta tuntuɓi wata ƴar jaridar ƙasar ta Senegal mai suna Sofia Ba wacce musulma ce kuma ita ce wakiliyar gidan talabijin na Poland a Afrika inda ta tabbatar wa da Alkalanci cewa labarin ƙarya ne.
Alkalanci ta ƙara da buƙatar ta data tuntuɓi ma’aikatar ilimi domin sanin sahihin labarin inda anan ma ta ƙara aikowa da Alkalanci cewa labarin ƙarya ne.
Babu dai wata sahihiyar kafar labarai data wallafa wannan labari a can Senegal da kuma wasu ƙasashe duk da cewa yana yaɗuwa a harshen Hausa da Turanci.
Sakamakon binciken:
La’akari da kasa samun wannan sanarwa ko labari a shafin ma’aikatar ilimi ta ƙasar Senegal tare da tabbacin da ma’aikatar ta bayyanawa Alkalanci ta hannun ƴar jarida a ƙasar mai suna Sofia Ba na cewa labarin ƙarya ne, kafar tantance labarai ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa labarin dake yaɗuwa cewa Senegal ta sanya Alkur’ani a cikin darasu a makarantun Senegal ƙarye ne.
