BindiddigiLabarin Makiyayi mai bindiga a Kasuwar Dawanau Ƙarya ne

Labarin Makiyayi mai bindiga a Kasuwar Dawanau Ƙarya ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa rashin samun tabbaci daga hukumomin tsaro da kuma rashin ganin rahoton a manyan gidajen jaridu masu inganci, Alkalanci ta yanke hukuncin cewa labarin da ke yawo game da wani makiyayi mai bindiga a kasuwar Dawanau da ke jahar Kano, ƙarya ne.

A ƙarshe-ƙarshen shekarar 2025 ne dai aka fara samun hare-haren yan fashin daji a wasu yankunan arewacin Kano.

Iƙirari:
Tun ranar Litinin 2 ga watan Fabrairun 2026, ake ta yaɗa jita-jita a shafukan sada zumunta da kuma gari cewa an ga wani makiyayi a kasuwar saida kayan abinci ta Dawanau ta jihar Kano ɗauke da bindiga a rataye yana tafiya da dabbobi. Wani shafin Facebook mai suna Adamu MB ya wallafa wani bidiyo dake wannan ikirari.

Wani shafin ma mai suna DOVE NEWS HAUSA shima ya wallafa wannan labari.

Wannan labarin ya haifar da firgici da rudani a tsakanin jama’a, inda aka ɗauka cewa masu garkuwa da mutane ne ko ‘yan bindiga ne suka shigo yankin.

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike na musamman don gano gaskiyar lamarin ta hanyar tuntuɓar hukuma da kuma duba sahihan majiyoyi.

Mun tuntuɓi daya daga cikin jami’an tsaro da ke aiki a ɗaya daga ofisoshin ‘yan sanda da ke jahar inda ya tabbatar mana ba shi da wannan labari ma gaba ɗaya. Sannan mun duba shafukan sada zumunta na hukumar ‘yan sanda, nan ma ba a wallafa wannan labari ba sannan babu wani sahihin gidan jarida kamar BBC ko Daily Trust da suka wallafa labarin.

A al’ada, idan irin wannan babban al’amari na tsaro ya faru a babbar kasuwa irin ta Dawanau, hukumomin tsaro sukan fitar da sanarwa ko kuma manyan jaridu su ɗauki rahoto, amma babu ko ɗaya daga ciki da ya tabbatar da hakan.

Sai dai binciken ya tabbatar da cewa wanda aka gani dauke da bindiga jami’in tsaro ne dake raka dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da rashin samun hujja daga hukumar ‘yan sanda da kuma rashin ganin labarin a sahihan kafafen yaɗa labarai, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan labari ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa wani labari ɗauke da hoton wani matashi inda yayi iƙirarin...

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya. Iƙirari: Akwai...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna...

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai babban birnin ƙasar Nijar, shugaban...

Karanta wannan

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar