Hukunci: Ƙarya ne
Kafar tantance labarai ta Alkalanci dai ta gano cewa sai idan ƙasashen biyu sun fita daga yarjejeniyar daƙile yaɗuwar makamin nukiliya ko kuma ƙasar Ukraine ta zama mamba ta ƙungiyar tsaro ta NATO ne ƙasashen Birtaniya da Faransa zasu iya bata makamin na nukiliya. Haka zalika babu inda Rasha ta bayyana Jamus a cikin jerin kasashen dake kokarin tallafa Ukraine mallakar Nukiliya. Ya zuwa yanzu dai babu wani sahihin dalili da zai sa ƙasashen na Turai su baiwa Ukraine makamin nukiliya.
Yayin da yaƙin da Rasha ke gudanarwa Ukraine ya shiga shekara huɗu akwai iƙirarai kala-kala dangane da yaƙin.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna WAT News Hausa ya wallafa wani labari dake cewa ƙasar Rasha na zargin ƙasashen Faransa da Birtaniya da yinƙurin baiwa Ukraine makamin nukiliya.

Shima wani shafin na Facebook mai suna Dove News Hausa ya wallafa irin wannan labari.

Wannan shafin kuma bidiyo ya wallafa tare da zargin Jamus da Faransa cewa suna ƙoƙarin taimakawa Ukraine ta sami makamin nukiliya.
Bincike:
Binciken Alkalanci ya gano cewa ƙasashen Faransa da Birtaniya na cikin ƙasashen da suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar daƙile yaɗuwar makamin nukiliya a duniya domin suna cikin ƙasashen dake da makamin.
Sannan binciken ya tabbatar da cewa ƙasar Ukraine bata da makamin nukiliya domin ta rabu da makamin tun shekarar 1994 bayan da akai zaman yarjejeniyar Budapest inda ƙasar Rasha da Birtaniya da Amurka suka yiwa Ukraine alƙawarin tsaro.
Tun shekarar 2022 ne dai Rasha ta fara zargin cewa Ukraine na yinƙurin mallakar makamin bam ɗin Nukiliya.
Ƙasashen Birtaniya da Faransa na cikin ƙasashen Turai dake kan gaba wajen yin Allah wadai da yaƙin da Rasha keyi a Ukraine tare da baiwa Ukraine kwarin gwiwa da tallafi.
A cikin bayanan da Rasha ta fitar dai tace ƙasar Jamus bata ciki masu ƙoƙarin bawa Ukraine tallafin Nukiliya.
Ƙasashen Turai kamar Faransa da Birtaniya na duba yiwuwar tura sojoji zuwa Ukraine domin tsaro, a ƴan kwanakin nan ne ma dai sojojin ƙasashen Turai suka gudanar da atisaye tare da takwarorin su na Ukraine inda sojin Ukraine sukayi galaba musamman kan yaƙi ta amfani da jirgi marar matuƙi.
Alkalanci ta gano sanarwar da ƙasashen biyu suka ƙaryata iƙirarin Rasha tare da ayyana shi a matsayin yaudara da yaɗa labaran ƙarya daga gwamnatin Rasha.
Sakamakon bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci dai ta gano cewa sai idan ƙasashen biyu sun fita daga yarjejeniyar daƙile yaɗuwar makamin nukiliya ko kuma ƙasar Ukraine ta zama mamba ta ƙungiyar tsaro ta NATO ne ƙasashen Birtaniya da Faransa zasu iya bata makamin na nukiliya. Haka zalika babu inda Rasha ta bayyana Jamus a cikin jerin kasashen dake kokarin tallafawa Ukraine mallakar Nukiliya. Ya zuwa yanzu dai babu wani sahihin dalili da zai sa ƙasashen na Turai su baiwa Ukraine makamin nukiliya.
