Hukunci: Ƙarya ne
Bisa ganin yadda labarin ya fara yaɗuwa a harshen turanci a ranar juma'a wanda a daren wannan rana shugaba Tinubu ya sha ruwa da ƴan majalisun tarayya, da kuma ka sa samun wata kafar yaɗa labarai data wallafa labarin cewa shugaban ya tafi Faransa ko wata kasa domin duba lafiyarsa, sannan ƙaryata labarin da Abdulazizz Abdulazizz mai magana yawun shugaban yayi, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa an tafi da shugaba Tinubu zuwa Faransa saboda cutar kansa ƙarya ne.
Ikirari:
Wani shafin Facebook mai suna MEDIA ADVERTS ya wallafa wani labari dake iƙirarin cewa an fitar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zuwa Faransa saboda cutar kansar sa tayi tsanani.
“Ciyon Cancer din Tinubu Yayi Tsanani An Fita Dashi Zuwa Faransa Da Gaugawa Domin Duba Lafiyar Sa. An Fidda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Zuwa Ƙasar Faransa, Domin Sake Duba Lafiyar Shi Cikin Gaggawa Yayin Da Likitocin Nasa Suka Tabbatar Cewa Ciwon Cancer Dinshi Yayi Tsanani Har Yakai Mataki Na Ukku A Wajan Magani.”

Wannan iƙirarin ya sami sama da tofa albarkacin baki dubu biyar tare da shares sama da ɗari huɗu da kuma likes kusan dubu shida.
Mutane da dama a comment section dai sun yarda da wannan labari kamar yadda kuke gani a ƙasa.

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta fara da duba shafukan masu magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu inda babu labarin tafiyar shi zuwa Faransa ko wata ƙasa a ranar juma’a ko ranar asabar.
Haka zalika Alkalanci ta duba sahihan kafafen yaɗa labarai da ke da wakilai a fadar shugaban ƙasa amma babu wannan labari na rashin lafiyar shugaban ƙasar balle batun tafiya da shi ƙasar Faransa.
Alkalanci ta ƙara da tuntuɓar Abdulaziz Abdulaziz mai magana da yawun shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu inda ya tabbatar wa da Alkalanci cewa wannan labari ƙarya ne;
“Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana Abuja cikin ƙoshin lafiya. Ko a jiya ya sha ruwa da ƴan majalisun tarayya kuma ya yi jawabi mai tsayi a wurin.”
Alkalanci ta sami wani ɓangare na jawabin shugaba Tinubu a shafin Bayo Onanuga babban mai magana da yawun shugaba Tinubu.
Wannan labari dai ya samo asali ne bayan da wani shafin X mai suna @MikeArnoldTruth ya wallafa iƙirarin ranar juma’a cewa shugaban na fama da cutar kansa da ta shiga babban mataki na uku.
Sakamakon binciken:
Bisa ganin yadda labarin ya fara yaɗuwa a harshen turanci a ranar juma’a wanda a daren wannan rana shugaba Tinubu ya sha ruwa da ƴan majalisun tarayya, da kuma ka sa samun wata kafar yaɗa labarai data wallafa labarin cewa shugaban ya tafi Faransa ko wata kasa domin duba lafiyarsa, sannan ƙaryata labarin da Abdulazizz Abdulazizz mai magana yawun shugaban yayi, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa an tafi da shugaba Tinubu zuwa Faransa saboda cutar kansa ƙarya ne.
