BindiddigiIna gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da...

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa rashin samun tabbaci daga hukumomin tsaro da kuma shaidar cewa bidiyon ba na Najeriya ba ne, Alkalanci ta yanke hukuncin cewa iƙirarin da ake yaɗawa a manhajar TikTok cewa jami’an tsaro sun ɗauke masu laifi daga Arewancin Najeriya zuwa Kudu, ƙarya ne.

Iƙirari
Wani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami’an tsaro sun kwashe waɗanda suka aikata laifi daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya. Masu yaɗa labarin suna cewa an yi hakan ne saboda ba a yanke hukunci ga masu laifi a Arewa.
Wannan jita-jita ta samo asali ne bayan faruwar wani mummunan al’amari a ranar 17 ga watan Janairu, 2026, inda wasu ɓata-gari a unguwar Chiranchi da ke garin Kano suka shiga wani gida tare da hallaka matar gidan da ‘ya’yanta shida.
Tun bayan faruwar wannan mummunan abin, ake ta yaɗa labaran ƙarya daban-daban a kan lamarin don haifar da ruɗani da tunzura jama’a.
Bincike da Bin diddigi:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike mai zurfi don gano gaskiyar lamarin ta hanyar tuntuɓar hukumomi da kuma yin binciken ƙwaƙwaf kan bidiyon da ake amfani da shi.
1. Tabbaci daga Hukumomi: Da farko, Alkalanci ta tuntuɓi wani sashe na jami’an da ke kula da al’amarin a hukumance. Sun tabbatar da cewa labarin ƙarya ne kuma babu wani shiri ko umarni na kwashe masu laifi daga Kano ko Arewa zuwa Kudancin Najeriya saboda dalilan da aka ambata.
2. Binciken Bidiyo da Kakin Jami’ai: Binciken fasaha da muka gudanar kan bidiyon ya nuna cewa asalin bidiyon ba a ƙasar Najeriya aka ɗauke shi ba bisa hujjoji da muka samu:
• Rubutun C.I.D: A cikin bidiyon da aka wallafa, mun gano cewa rigar da jami’in ‘yan sanda da ya taso ƙeyar mai laifi a bidiyon yake sanye da ita, tana da rubutun (C.I.D) a baya kuma tana da launin shuɗi mai duhu. Tsarin zubin kakin ‘yan sanda da jami’an Najeriya ke sanyawa babu irin wannan rubutun a baya.

Hoton bidiyon dake yaduwa



• Asalin Kakin: Bincikenmu ya gano cewa jami’an tsaron ƙasar Ghana ne ke amfani da wannan kakin. Hakan ya yi daidai da wata sanarwa da hukumar ‘yan sandan ƙasar Ghana ta fitar tun a shekarar 2020, inda ta umarci jami’anta da su riƙa sanya kakin nasu, wanda ya haɗa da wannan riga da aka gani a bidiyon.

Hoton sanarwar hukumar kula da ‘yan sanda ta Ghana da tayi



• Kwatancen Hotuna: Har ila yau, a wasu hotuna da aka wallafa a ƙasar ta Ghana, an samu wani jami’in sanye da irin wannan riga sak, wanda ke tabbatar da cewa bidiyon ba shi da alaka da Najeriya.
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da shaidar cewa bidiyon na jami’an tsaron Ghana ne ba na Najeriya ba, da kuma tabbacin da aka samu daga jami’an tsaro na Najeriya cewa ba a ɗau irin wannan mataki ba, Alkalanci ta tabbatar da cewa labarin da ake yaɗawa cewa an kwashe masu laifi daga Kano zuwa Kudu ƙarya ce tsagoronta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa wani labari ɗauke da hoton wani matashi inda yayi iƙirarin...

Labarin Makiyayi mai bindiga a Kasuwar Dawanau Ƙarya ne

A ƙarshe-ƙarshen shekarar 2025 ne dai aka fara samun hare-haren yan fashin daji a wasu yankunan arewacin Kano.Iƙirari:Tun ranar...

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya. Iƙirari: Akwai...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna...

Karanta wannan

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar