Fayyace abubuwaIna gaskiyar cewa Rasha bata ɗaukar ƴan Najeriya aikin...

Ina gaskiyar cewa Rasha bata ɗaukar ƴan Najeriya aikin soja?

-

Yayin da yaƙin da Rasha keyi a ƙasar Ukraine ke cika shekaru huɗu wanda ya haddasa mutuwar ɗaruruwan mutane.
Tunda yaƙin ya shiga shekara ta biyu ne dai ake zargin Rasha da ɗaukar ƴan Afrika tana tura su fagen fama ba tare da cikakken horo ba, kuma babu wani tsari na biyan iyalai diyya ko inshora.
Akwai dai gidajen jaridu da dama da suka rawaito mutuwar ƴan Afrika yayin da suke taya Rasha yaƙi a Ukraine.
A farko-farkon shekarar 2026 ne dai labarin mutuwar wasu ƴan Najeriya ya yaɗu matuƙa a kafafen watsa labarai bayan da iyalan su suka faɗi yadda aka yaudare su shiga sojan Rasha.
Jakadan ƙasar Rasha a Najeriya ya musanta wannan labari tare da cewa ƙasar sa bata ɗaukar matasan Najeriya a Rasha balle ta tura su fagen fama.
Ya bayyana cewa a hukumance basu da masaniya kan wannan batu.
Bincike:
A ranar Alhamis 4 ga watan Janairun shekarar 2024 shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya fitar da wata doka ta musamman da ta sahale a baiwa duk wani ɗan ƙasar waje da iyalansa zama ƴan ƙasa.
Dokar ta bada umarnin cewa duk wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikin soji na aƙalla shekara ɗaya a bashi shi da iyalansa da iyayen sa Fasfo.
A watan Nuwamba shekarar 2024 mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Rasha Irina Volk ya bayyana yadda sama da ƴan ƙasar waje 3,300 suka zama ƴan ƙasa saboda yaƙin da suka yi da Ukraine, kamar yadda jaridar ƙasar Rasha mai suna The Moscow Times to rawaito.
Akwai wani dan Najeriya mai suna Abubakar Adamu da tuni ya bayyana kokensa tare rokon hukumomin Najeriya dasu dawo dashi gida daga Rasha tare da bayyana cewa yaudarar sa akayi. kamar yadda zagazola Makama ya rawaito.
Akwai wani matashi mai suna Balogun Ridwan wanda dan Najeriya ne da sojojin Ukraine suka kama yana taya Rasha yaki a Ukraine. Shima ya bayyana yadda aka yaudare shi da cewa ya sami aikin injiniya a Rasha amma da ya je aka tura shi aikin soja.
Sannan a tsarin kasar Rasha shiga aikin soja abune na shiga yarjejeniya da gwamnatin kasar domin kare iyakokin kasar wanda yasa babu wanda zai shiga aikin soja a tura shi fagen yaki ba tare da sanin gwamnati da manyan sojin kasar ba.
A watan Yunin shekarar 2025 editan Alkalanci ya ziyarci ƙasar Ukraine inda ya gana da wasu fursunonin yaƙi da suka haɗa da ƴan Afrika.
Sun bayyana yadda aka yaudare su tare da tura su fagen yaƙi.
Akwai dai ƴan Najeriya da suke a hannun hukumomin Ukraine a matsayin fursunonin yaƙi bayan da aka kamasu suna taya Rasha yaƙi.
Ma’aikatar harkokin Wajen Najeriya ta gargaɗi ƴan ƙasar da su guji zuwa wasu ƙasashe domin zama sojojin haya musamman yadda ake yaudarar su da kuma sanya hannu cikin yarjejeniyar da ba a yaren da suke fahimta ba.
Binciken Alkalanci ya gano cewa dokar shiga sojan Rasha tsakanin mutum ne da gwamnatin ƙasar ba wasu mutane gama gari ba.
Wanda ya tabbatar da cewa duk ƴan Najeriyar da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga aikin soja tare da tura su fagen yaƙi akwai masaniyar manyan jami’an gwamnati da na sojin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Logged in as Alhassan Bala. Log out?

Please enter your comment!

Sababbin Labarai

Ziyara zuwa Birtaniya: Me yasa Tinubu ya zama na farko cikin shekaru 37 duk da ziyarar da Yar’adua ya kai?

Bayan da labarin ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu zuwa Birtaniya ta yaɗu gidajen labarai ke bayyana cewa wannan irin...

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa wani labari ɗauke da hoton wani matashi inda yayi iƙirarin...

Labarin Makiyayi mai bindiga a Kasuwar Dawanau Ƙarya ne

A ƙarshe-ƙarshen shekarar 2025 ne dai aka fara samun hare-haren yan fashin daji a wasu yankunan arewacin Kano.Iƙirari:Tun ranar...

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi...

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya. Iƙirari: Akwai...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna...

Karanta wannan

Hoton matashin da ake Iƙirarin EFCC ta cafke kan kudin masallaci karya ne

Iƙirari: Wani shafin Facebook mai suna A Fayyace ya wallafa...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar

Skip to toolbar