BindiddigiIna gaskiyar cewa babu sojin ƙasar waje a Nijar

Ina gaskiyar cewa babu sojin ƙasar waje a Nijar

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun inda hukumomin Nijar da Rasha suka bayyana ficewar sojin da suka zo Nijar shekarar data gabata suka kuma maye gurbin sansanin sojin Amurka, Sannan ƴan jaridu da mutanen a garin Tilliberi sun tabbatar da ganin sojin Rasha lokacin da shugaban ƙasar Nijar Tiani yakai ziyara. Haka zalika an gano sojin ƙasashen waje a bidiyon taron yaye sojojin ƙasar ta Nijar a satin daya gabata. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin babu sojin ƙasashen waje a Nijar jirkata bayani ne wato misleading a turance.

Juyin mulkin da soji sukayi a ƙasar Nijar ya janyo takun saƙa da wasu ƙasashe.

Ƙasar ta Nijar dai ta fice daga ƙungiyar ECOWAS tare da korar sojin ƙasashen Faransa da Amurka.

Nijar dai ta ƙarfafa alaƙa da ƙasar Rasha tare da karbar sojojin na Rasha bayan ficewar na Faransa da Amurka.

An dai rawaito yadda sojin kasar ta Rasha suka maye gurbin sojin Amurka a sansanin sojin da suka zauna na shekaru da dama.

Ikirari:

Wasu shafukan sada zumunta sun rawaito Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine yayi ikirarin cewa babu wani sojan kasar waje a kasar ta Nijar a yanzu haka. Yayi wannan jawabi  ne a birnin Dakar babban birinin kasar Senagal.

Wani shafin Facebook mai suna Nijer 24 ya wallafa wannan ikirari.

Shima wani shafi mai suna Niger 227 post Tv  ya wallafa wannan ikirarin.

Hoton labarin da aka jirkita kuma yake cigaba da yaduwa

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa sojojin kasar Rasha sun sauka kasar Nijar a ranar 4/12/2024 kaamar yadda hukumar tsaro ta Rasha a Africa mai suna The Africa Corps ta wallafa a shafin ta na X(Twitter).

Haka zalika a watan mayun shekarar da ta gabata kafar dillancin labarai ta Reuters ta rawaito cewa sojojin kasar Rasha sun maye gurbin dakarun sojin Amurka a sansanin da suka zauna.

A watan Mayu ne dai kasar ta Nijar ta fice daga yarjejeniyar tattara bayanan tsaro da Rasha da Turkiyya.

Duk da wadannan bayanai dai binciken Alkalanci ya tabbatar da cewa har zuwa watan Oktoba akwai sojojin ƙasar Rasha a ƙasar Nijar, domin an hangesu a bidiyon da kafafen yada labaran kasar suka wallafa na yaye sojoji a Tilliberi da kuma lokacin da shugaban Nijar Tiani ya ziyarci Tilliberi.

Ya zuwa yanzu duk da girman ficewar sojin ƙasashen waje, Nijar da Rasha basu bayyana ficewar dakarun sojin Rasha daga Nijar ba.

Sakamakon bincike:

Bisa kasa samun inda hukumomin Nijar da Rasha suka bayyana ficewar sojin da suka zo Nijar shekarar data gabata suka kuma maye gurbin sansanin sojin Amurka, Sannan ƴan jaridu da mutanen a garin Tilliberi sun tabbatar da ganin sojin Rasha lokacin da shugaban ƙasar Nijar Tiani yakai ziyara. Haka zalika an gano sojin ƙasashen waje a bidiyon taron yaye sojojin ƙasar ta Nijar a satin daya gabata. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin babu sojin ƙasashen waje a Nijar jirkata bayani ne wato misleading a turance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar