Shugaba Bola Tinubu a cikin jawabinsa na ranar daya ga watan Oktoba wato ranar bikin yan cin kan kasar yayi ikirarin cewa cikin shekara guda na mulkinsa kasar ta sami shigowar masu zuba jari daga kasashen waje daya kai sama da dala biliyan talatin $30bn.
Hukumar kididdiga ta kasar wato NBS takan fitar da yawan kudaden da suka shigo Najeriya duk watanni uku wato kwata wanda ya hada da saka hannun jari daga kasashen waje.
A farkon watanni uku na wannan shekara ta 2024, Najeriya ta sami shigowar kudade daga masu sanya hannun jari da suka kai dala miliyan $119.18m a yayin da a tsakanin Afrilu zuwa Satumba kuma kasar ta sami shigowar dala miliyan $183.97. Haka zalika a watanni ukun karshen shekarar 2023 kuwa kasar ta sami shigowar dala miliyan $59.77m a inda watanni Yuli, Agusta da satumbar 2023 kuwa kasar ta sami shigowar kudaden zuba jari dala $86.03 wato watannin da Tinubu ya karbi mulki kenan.
Idan aka lissafa kididdiga daga hukumar ta NBS za’a iya cewa daga watan Afrilun 2023 zuwa watan Maris din 2024 kudin zuba jari daga kasashen waje zai tashi dala miliyan $448.95m wanda bai kai ko rabin biliyan dala daya ba.
Haka zalika babu wata shaida Ko alkaluma dake nuna cewa kasar ta sami shigowar kudaden zuba jari da suka kai dala biliyan $30bn a tsakanin watanni shida zuwa watanni tara na wannan shekarar ta 2024.
Sannan a cikin jawabin Tinubu yayi ikirarin cewa ya gaji dala biliyan $33bn a asusun ajiyar kasar wato foreign reserve. To sai dai alkaluma daga baban bankin kasar ya nuna cewa abinda ya gada daga Muhammadu Buhari yafi haka domin kuwa an bar masa dala biliyan $35bn maimakon $33billion da yayi ikirari.
Iƙirarin na shugaba Tinubu dai ba gaskiya bane. Wato a turance ake cewa misleading Ko incorrect.