Abinda muke a Alkalanci (What we do at Alkalanci)
Abinda Alkalanci yake yi shine na ƙoƙarin bindiddigin iƙirari, bayani, hotuna dama bidiyo domin yaƙi da bayanai, ko alƙaluman ƙarya da na shaci faɗi wato misinformation/disinformation a turance. Sannan muna ilimantar da mutane da koyar dasu dabarun kaucewa labaran ƙarya da samun sahihan bayani musamman a wannan lokaci da ake samun ƙarin bayanai, hotuna da bidiyon ƙarya.
Abunda muke fata shine mu zama mun shahara a matsayin kafa ta tantance labarai, bindiddigi, bincike wato fact-checking da kuma ilimin samun sahihan labarai wato media literacy domin yaƙi da labaran da ba gaskiya ba. Mu kuma zama zakaran gwajin dafi wajen fito da sabbin hanyoyin kare kai daga labaran ƙarya a harshen Hausa.
Tsarin Hukunci
A Alkalanci, Muna amfani da matakai wajen bayyana sakamakon binciken abinda muka tantance. Bayan kammala bincike muna yanke hukunci bisa la’akari tare da amfani da bayanai na gaskiya da muka gano.
Hukuncin da muke amfani dasu sune kamar haka:
1. Gaskiya ne: Idan bayanai da alƙaluman sun bayyana cewa iƙirarin gaskiya ne.
2. Ƙarya ne: Idan bayanai da alkaluma sun nuna ba haka abin da akai iƙirari yake ba.
3. Ƙamshin Gaskiya: Idan iƙirarin akwai wasu sashe da suke gaskiya ne, amma aka sauya bayanin don wata manufa.
Ta yadda muke zabar iƙirari don tantancewa (How we choose claims to fact-check)
A Alkalanci, muna neman iƙirari ta hanyar bibiyar kafafen sada zumunta, gidajen jaridu, da kalamai da kai a kafafen sadarwa na zamani, takardun manema labarai, rahoto da sauran su. Haka zalika masu bibiyarmu na turo mana da iƙirari ta lambar WhatsApp ɗinmu +234 701 030 6604 ko email: [email protected]
Kasancewar baza mu iya tantance ko bincikar dukkan iƙirari ba, muna zaɓar waɗanda suka fi muhimmanci ta hanyar amsa waɗannan tambayoyi dake ƙasa:
a. Zamu iya tantance bayanin? Domin bama tantance ra’ayin mutane.
b. Akwai tababa kan iƙirarin inda wasu ke ganin gaskiya ne wasu kuma na ganin ƙarya ne?
c. Shin bayanin na iya haddasa matsala ko cutar wa Idan ƙarya ne?
d. Shin iƙirarin na yaɗuwa kamar wutar daji, ko kuma akwai yiwuwar ya yaɗu kamar wutar daji?
Yadda muke gyara kura-kurai (How we correct our mistakes)
Manufar mu ita ce ta samar da sahihan bayanai. Don haka da zarar kunga wani kuskure a rahoton mu kada kuyi ƙasa a gwiwa wajen tuntubarmu ta email ɗin Edita a [email protected]
Zamu ƙara duba labarin tare da gyara shi inda ya dace.
Idan munyi wani babban kuskure zamu gyara nan take tare da rubuta “BAYANIN EDITA” ko “GYARA” tare da bayyana inda mukai gyaran da kuma samar da bayanan da suka dace a gurin.
Ida har gyaran ya kai ga canza hukuncin da muka yi zamu rubuta bayanin a saman rahoton. Wasu lokuta mukan ƙara abubuwa a rahoto ba don gyara ba sai don ƙara bayanai wanda zamu rubuta don masu karatu.