BindiddigiBincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la’akari da cewa bidiyon na ɗauke da alamun sarrafa na’ura (AI), da kuma rashin gaskiyar kalaman idan aka kwatanta da asalin hirar, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan bidiyon ƙarya ne da aka ƙirƙira.


Iƙirari:

A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda ke nuna Alhaji Ali Baba Fagge, tsohon mai ba wa gwamna shawara kan harkokin addini a gwamnatin tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

A cikin bidiyon, ana jin muryar ɗan siyasan yana furta wasu kalamai  inda aka sanya hoton matar tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, kuma aka rubuta cewa “Ali Baba yabar APC…” a cikin bidiyon mai tsawan sakan ashirin da tara, anji yana cewa; “Billahillazi la’ilaha illahuwa na dauke ki munyi wata shida dake, ke daduro na ce, ke karuwa ta ce, ni mai cin amana ne, kuma fasiki ne, kuma makaryaci da tumasanci...

Wannan bidiyo ya bayyana ne kwanaki kaɗan bayan  Ali Baba Fagge ya yi wata tattaunawa ta siyasa da gidan radiyo na Express, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike na musamman kan wannan bidiyo.

Da farko, Alkalanci ta samo asalin hirar da Alhaji Ali Baba Fagge ya yi da gidan Radiyon Express a makon da ya gabata. Binciken ya tabbatar da cewa duk da ya yi martani irin na siyasa, babu inda ya furta wadancan kalamai na sabon bidiyon.

Na biyu, ta hanyar amfani da fasahar gano bidiyo da hotuna hadin AI mai suna AI Video Detector sakamakon ya bayyanawa Alkalanci cewa bidiyon da ke yawo a TikTok haɗin AI ne (Deepfake).

Sannan Alkalanvi ta fahimci masu yaɗa labarin sun yi amfani da fasahar kwaikwayon murya da motsin baki (lip-sync technology) don sanya ɗan siyasan faɗar abin da bai furta ba kuma alamu sun nuna cewa sun yayyanke asalin maganar.

Sakamakon Bincike:

Bisa la’akari da cewa bidiyon na ɗauke da alamun sarrafa na’ura (AI), da kuma rashin gaskiyar kalaman idan aka kwatanta da asalin hirar, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan bidiyon ƙarya ne da aka ƙirƙira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Wasu shafukan da suka dinga yaɗa ƙage da labaran ƙarya a shekarar 2025

Shekarar 2025 dai ta kasance shekarar da aka sami wasu shafukan sada zumunta da kaso mafi yawa na abubuwan...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar