BindiddigiBidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne,...

Bidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne, bidiyon ya faru a Ghana ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano tambarin yan sandan Ghana, da kuma lambar kira don agajin gaggawa ta Ghana a bidiyon dake yaduwa wanda ya tabbatar da cewa ba’a Edo bane.

 

A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na amfani da wannan dama wajen yaɗa labarai, hotuna da bidiyon ƙarya kan abun.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Abumusa’ab J Aliyu ya wallafa wani rubuta da faifan bidiyo dake cewa
“Hukumomi Sun Fara Kama Matsiyatan da Suka Yiwa Yan Uwanmu Hausawa Matafiya Kisan Gilla A Jihar Edo…”
Hoton bidiyon karya dake cigaba da yaduwa
Shima wani shafin na facebook mai suna Nasiru Ibrahim Babajo ya wallafa irin wannan bidiyo inda ya rubuta cewa;
“Alhamdulillah An cigaba da kama yan lskan da suka yiwa Yan Arewa k!ssan gilla a Jihar Edo.”
Hoton post din karya dake cigaba da yaduwa
Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba shafin rundunar ƴan sanda Najeriya inda ta tabbatar da kama mutum goma sha huɗu da ake zargi da hannu wajen kisan to amma babu hoto ko bidiyo.
Alkalanci ta duba wannan bidiyo da idon basira tare da gano tambarin ƴan sanda ƙasar Ghana a jikin rigunan ƴan sandan.
Haka zalika a jikin motar ƴan sandan an  rubuta lambar 191 da 18555 waɗanda lambobin kiran ƴan sanda domin agajin gaggawa na ƙasar Ghana ne.
Hoton sashen dake nuna lambar yan sandan Ghana a bidiyon
Lambar kira domin agajin gaggawa a Najeriya 112 ce.
Sakamakon bincike:
Bisa la’akari da kayan ƴan sanda da aka gani a bidiyon, tambarin dake ɗauke da Ghana, da kuma lambar neman agajin ƴan sandan ƙasar Ghana a jikin motar ƴan sandan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa bidiyon kame ne da ƴan sandan Nijeriya sukayi a Edo ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar