BindiddigiƘarya ne: Shugaba Tinubu bai baiwa iyalan marigayi Yar'adua...

Ƙarya ne: Shugaba Tinubu bai baiwa iyalan marigayi Yar’adua bashin Dala biliyan 5 ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun wannan labari a shafukan shugaban ƙasa Tinubu, da sauran sahihan gidajen jaridu, tare da gano cewa lokaci na ƙarshe da Tinubu ya ambaci sunan tsohon shugaban ƙasa marigayi Yar'adua shine a watan Mayun shekarar 2023. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa; Tinubu yace ya kamata iyalan Yar'adua su fi kowane mutum a Najeriya jin daɗi, hakan yasa na basu bashin billion 5 Naira sai nan da shekara ɗari su biya" Ƙarya ne.
Akwai wani iƙirari dake yaɗuwa matuƙa a shafukan sada zumunta dangane da iyalan tsohon shugaban ƙasar Najeriya marigayi Umaru Musa Yar’adua.
Iƙirari:
Wani shafin Tiktok mai suna Malam Khan ya wallafa wani iƙirari dake cewa; “Tinubu yace  ya kamata iyalan Yar’adua su fi kowane mutum a Najeriya jin daɗi, hakan yasa na basu bashin billion 5 Naira sai nan da shekara ɗari su biya.”
Wanna wallafa ta sami mutane da dama da suka tofa albarkacin baki tare da kara wallafa ta.
Labaran karya ake yaduwa kan iyalan Yaradua
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta fara da duba shafukan sada zumuntar shugaban ƙasa Bola Tinubu don ganin wannan labari amma babu wani abu makamancin hakan. Binciken Alkalanci ya gano cewa lokaci na ƙarshe da Tinubu ya ambaci sunan tsohon shugaban ƙasar Najeriya marigayi Umaru Musa Yar’adua shine a watan Mayun shekarar 2023.
Kuma a wancan lokaci yana magana ne kan tunawa da marigayin tare da alkawarin yin shugaban ci irin nashi, hakan ya faru ne kafin a rantsar dashi Tinubu.
Alkalanci ta ƙara da bincika ko akwai wata sahihiyar kafar yaɗa labarai data rawaito wannan labari amma babu, duk da girman sa.
Sannan kafar tantance labarai ta Alkalanci ta aika sakon tuntuɓa don jin inda mai shafin Tiktok ɗin don jin inda ya samo labarin to amma bayan ya karanta sama da awanni  kusan 24 bai amsa ba.
Sakon da Alkalanci ta tura ba tare da samun amsa ba
Mun ajiye wannan ikirari wanda zaku iya gani koda wanda ya wallafa ya goge a nan.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun wannan labari a shafukan shugaban ƙasa Tinubu, da sauran sahihan gidajen jaridu, tare da gano cewa lokaci na ƙarshe da Tinubu ya ambaci sunan tsohon shugaban ƙasa marigayi Yar’adua shine a watan Mayun shekarar 2023. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa; Tinubu yace ya kamata iyalan Yar’adua su fi kowane mutum a Najeriya jin daɗi, hakan yasa na basu bashin billion 5 Naira sai nan da shekara ɗari su biya” Ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar